Sojoji Sun Yi Kofar Rago ga Bello Turji, Ana Kokarin Cafke Shi

Sojoji Sun Yi Kofar Rago ga Bello Turji, Ana Kokarin Cafke Shi

  • Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa ya ce an kashe na hannun daman Bello Turji, kuma sauran abokan huldarsa sun shiga hannu
  • Sojoji na ci gaba da gudanar da hare-hare domin kama Bello Turji, wanda ya addabi jihohin Sokoto, Zamfara, Kebbi da kewayensu da ta'addanci
  • Janar Musa ya ce sama da 'yan ta'adda 120,000 sun mika wuya a yankin Arewa yayin da ake cigaba da ware wadanda aka tilastawa shiga ta'addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya sha alwashin kama babban dan ta'adda, Bello Turji, da ya shahara da ta'addanci a Sokoto, Zamfara, da Kebbi.

Janar Musa ya ce kama Turji abu ne da lokaci kawai ya rage, domin sojoji na ci gaba da gudanar da tsare-tsare wajen ganin hakan.

Kara karanta wannan

An kama 'yan fashi 189, masu garkuwa 39 da 'yan daba 1,987 a Kano

Janar Musa
Sojoji sun sha alwashin kama Turji. Hoto: Defence Headquaters
Asali: Facebook

Da yake magana a wani shiri na musamman da aka watsa a tashar Channels Television, Janar Musa ya ce 'yan ta'adda da dama sun mika wuya a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kashe na hannun daman Bello Turji

Babban Hafsan Tsaro, Janar Musa, ya ce an yi nasarar kakkabe dukkan kwamandojin Bello Turji da suka rika taimaka masa wajen gudanar da ta'addanci a Arewa maso Yamma.

“Tun da ya fahimci cewa muna bibiyarsa, sai ya fara buya amma muna ci gaba da gudanar da aiki a kansa.
Muna kama duk wanda ke kusa da shi, kuma mun kashe kwamandojinsa.”

- Janar Christopher Musa

Sojoji na gudanar da hare-hare kan duk masu bayar da goyon baya ga Turji a jihohin Sokoto, Zamfara, da Kebbi, domin tabbatar da cewa ya rasa mafaka ko taimako daga kowane bangare.

Sama da 'yan ta'adda 120,000 sun mika wuya

Kara karanta wannan

'Gawa ta ƙi rami': Hedikwatar tsaro ta fadi shirinta na kawo ƙarshen Bello Turji

Daily Post ta wallafa cewa Janar Musa ya bayyana cewa sama da 'yan ta'adda 120,000 sun ajiye makamansu a Arewa maso Gabas.

Ya kuma tabbatar da cewa ana ci gaba da tantance wadanda aka tilasta shiga ta'addanci da kuma masu hannu kai tsaye a ayyukan barna.

Hafsan tsaron ya ce;

“Muna gudanar da bincike mai zurfi don rarrabe wadanda aka tilastawa shiga ta'addanci daga wadanda suka zama manyan masu shirya munanan ayyukan.”

Ya jaddada cewa masu hannu wajen haddasa tashin hankali da kashe-kashe za su fuskanci hukunci mai tsanani domin tabbatar da adalci ga al'umma da kuma tsaron kasa baki daya.

An kama masu laifi sama da 2,000 a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta fitar da rahoton karshen shekara kan nasarar da ta samu a 2024.

Legit ta rahoto cewa 'yan sandan Kano sun yi nasarar kama masu laifi da dama da suka hada da masu garkuwa, 'yan fashi, barayi da sauransu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng