Awanni da Sukar Kudirin Harajin Tinubu, Abba Gida Gida Ya Gana da Shugaban Kasa
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf tare da takwarorinsa sun ziyarci shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a gidansa
- Gwamnonin sun kai ziyarar a ranar 1 Janairu, 2025 ne domin taya shugaba Tinubu murnar ganin sabuwar shekara
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi amfani da damar wajen tunatar da Tinubu muhimmancin kara habaka tattalin arzikin Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mika sakon taya murna ga Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu a kan shiga sabuwar shekara ta 2025.
Gwamnonin sun ziyarci gidan Shugaban Kasa a Lagos a ranar Laraba 1 Janairu, 2025 domin mika sakon taya murnar kafa da kafa ga Tinubu.
A cikin wata sanarwa da Daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, a shafin Facebook, Gwamna Yusuf ya hadu da takwarorinsa wajen kai gaisuwar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun isa gidan Tinubu karkashin jagorancin Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Dr. Abdulrazaq Abdulrahman, inda su ka bayyana fatansu na samun karin ci gaba.
Abba ya mika bukatar Kano ga Tinubu
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya bukaci shugaba Tinubu da ya kara mayar da hankali wajen samar da ribar dimokuradiyya ga jihar Kano.
Ya ce hakan ya na da muhimmanci kwarai duba da matsayin jihar na daya daga cikin jihohin da suka fi yawan jama’a da muhimmanci tattalin arziki a Najeriya.
”A zuba hannun jari a jihar Kano,’’ Abba
Gwamnatin Kano ta ce akwai bukatar kara zuba jari a fannin ci gaban ababen more rayuwa, yana mai cewa irin wadannan jarin za su canza fasalin jihar.
Gwamna Yusuf ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na yin aiki kafada da kafada da gwamnatin tarayya don tabbatar da cewa al’ummar Kano sun ci gajiyar mulki.
Ya bayyana ccewa akwai bukatar jama’a su sharbi romon dimukuradiyya, musamman a fannonin ababen more rayuwa, ilimi, lafiya, da damammakin tattalin arziki.
Gwanatin Kano ta soki kudirin harajin Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sake sukar kudirin harajin gwanatin Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce zai rarraba kawunan 'yan kasa
Injiniya Abba Kabir Yusuf, wanda ya ga rashin dacewar sauye-sauyen harajin a lokacin da 'yan kasa ke fama da matsananciyar wahala, ya shawarci gwamnati kan ceto jama'a daga talauci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng