An Shiga cikin Alhini da Gwamna Bala Ya Yi Babban Rashi a Rayuwarsa

An Shiga cikin Alhini da Gwamna Bala Ya Yi Babban Rashi a Rayuwarsa

  • Yadikkon Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, Hauwa Duguri ta rasu a ranar 1 ga Janairu 2025 tana da shekaru 120 da haihuwa
  • Mai ba da shawara kan harkokin yada labarai na gwamna, Mukhtar Gidado, ya bayyana mutuwar Hauwa a matsayin babban rashi
  • An shirya yin sallar jana’iza a filin taro na Dr. Rilwan Adamu a fadar Gwamnatin jihar Bauchi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi - An shiga alhini bayan mutuwar yadikkon Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi.

Marigayiyar mai suna Hauwa Duguri, ta rasu ne a yau Laraba 1 ga watan Janairun 2024 tana da shekaru 120.

Gwamna Bala ya tafka babban rashi
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya rasa yadikkonsa. Hoto: Sen. Bala Mohammed.
Asali: Twitter

Gwamna Bala ya rasa kishiyar mahaifiyarsa

Mai ba da shawara kan harkokin yada labarai na Gwamnan Bauchi, Mukhtar Gidado shi ya sanar da rasuwar a cikin wata sanarwa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Kotu a amince da tsare shugabannin Miyetti Allah na kwanaki 60

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gidado ya ce marigayiyar da ake kira Dada ta kasance kishiyar mahaifiyar Gwamna Bala Mohammed ce.

“Hauwa Duguri, wadda ake kira Dada, kishiyar mahaifiyar Gwamna Bala Mohammed ce, tana da matsayi na musamman a cikin al’umma.”
“Wannan fitacciyar uwa ta rasu ne a ranar 1 ga Janairu 2025, tana da shekaru 120 da haihuwa, bayan ta yi rayuwa mai cike da albarka.”

- Mukhtar Gidado

Yaushe za a yi sallar jana'izar marigayiyar?

Gidado ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi da karshen nuna kulawa da tausayi da kuma hidimar addini da take yi a rayuwarta.

Ya ce za a gudanar da sallar jana’iza a filin taro na Dr. Rilwan Adamu da ke Fadar Gwamnatin jihar Bauchi.

A cewar Gidado, Gwamna Bala Mohammed ya nuna jimami ga dukkan dangin Duguri da kuma wadanda suka san wannan uwa mai daraja.

Ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da ya sanya ta cikin Aljannar Firdausi tare da ba wa danginta ƙarfin zuciya wajen jure wannan babban rashi.

Kara karanta wannan

Rai baƙon duniya: Kwamishina mai ci a Najeriya ta riga mu gidan gaskiya

Kwamishina a jihar Bayelsa ta rasu

Kun ji cewa Gwamnatin Bayelsa ta sanar da rasuwar Kwamishinar Harkokin Mata, Elizabeth Bidei, mamba a majalisar zartarwa.

Sanarwar gwamnatin jihar ta nuna alhini ga iyalan marigayiyar, musamman mijinta, Cif Jackson Bidei da 'ya'yansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.