Yadda Bola Tinubu Ya Fara Fuskantar Babbar Matsala da Barazana kan Kudirin Haraji
- Daniel Bwala ya yi zargin cewa akwai waɗanda suka fara yi wa shugaban ƙasa, Bola Tinubu barazana kan kudirin haraji
- Hadimin shugaban ƙasar ya ce ya kamata gwamnonin da ba su yarda da kudirin ba su tuntuɓi ƴan majalisar tarayya na jihohinsu
- Ya kuma musanta ikirarin Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi cewa shugaban ƙasa ba ya sauraren koken jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsare-tsaren sadarwa, Daniel Bwala ya yi zargin cewa ana shafawa Bola Tinubu baƙin fenti kan kudirin haraji.
Bwala ya ja hankali da cewa har yanzu kudurin na gaban Majalisa bai riga da ya zama doka ba, duk gwamnan da ke ganin akwai matsala ya tuntuɓi ƴan majalisar jiharsa.
Hadimin shugaban kasar ya yi wannan furucin ne a wata hira da gidan talabijin na Channels tv ranar Laraba, 1 ga watan Janairu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nista Daniel Bwala ya kare shugaban ƙasa Bola Tinubu da cewa ba ya ɓangaren gwamnatin da aka ɗorawa haƙƙin yin dokoki.
Bola Tinubu na sauraren koken jama'a
Da yake martani ga kalaman Gwamnan Bauchi, Bwala ya ce:
"Inda ban yarda da shi (gwamnan Bauchi) ba shi ne da ya ce shugaban ƙasa ba ya sauraren koke, idan wasu gwamnoni ba su iya sa shugaban ya yi abin da suke so ba, hakan ba yana nufin ba ya sauraren koke ba ne."
"Saboda gwamnoni 37 gare mu har da ministan Abuja, ƴan Najeriya sun haura miliyan 200. Ina ganin maimakon surutu da yi wa shugaban kasa zagon kasa, ya kamata gwamnoni su yi magana da ‘yan majalisarsu.
"Dimokuraɗiyya ce, ya gabatar da ƙudirorin ga majalisar dokoki ta ƙasa, ita ke da alhakin tattaunawa kuma ta yi abin da ya dace kafin amincewa da su.
Ana yi wa Bola Tinubu barazana
Bwala ya shawarci gwamnonin da ke adawa da kudirin harajin su zauna da ƴan majalisar tarayya na jihohinsu domin gabatar da kokensu, Vanguard ta ruwaito.
"Duk gwamna da ke ganin akwai damuwa, ya tuntuɓu 'yan majalisar dokoki na jiharsa don su gabatar da damuwarsa a majalisar dokoki ta ƙasa. A ƙarshe, matakin 'yan majalisar zai yanke hukunci.
“Na yi imani cewa mutane da yawa suna yi wa shugaban ƙasa barazana, kuma ba zan ambaci kowa ba," in ji shi.
NLC ta nanata kiran a janye kudirin haraji
Kun ji cewa kungiyar kwadago ta Najeriya watau NLC ta dage cewa ya kamata Bola Tinubu ya janye kudirin gyara. haraji daga Majalisar tarayya.
A sakon murnar shigowa sabuwar shekara, NLC ta ce kudirin zai kata jefa m'sikata cikin kunci da wahalhalun rayuwa bayan wanda ake fama da su.
Asali: Legit.ng