Kotu Ta Yi Hukunci kan Mahadi Shehu kan Zargi game da Sojojin Faransa, Ta Fadi Dalili

Kotu Ta Yi Hukunci kan Mahadi Shehu kan Zargi game da Sojojin Faransa, Ta Fadi Dalili

  • An gurfanar da mai fashin baki, Mahadi Shehu a gaban kotun majistare a Kaduna bisa zargin hada baki, tallafa wa ta'addanci, da tayar da rikici
  • Alkalin kotun, Abubakar Lamido, ya tura Mahadi Shehu gidan gyaran hali har zuwa 14 ga watan Janairun 2025 domin cigaba da sauraron shari'ar
  • Zargin Mahadi Shehu ya danganci wallafa bayanin karya kan kafa sansanin sojin Faransa a Arewa maso Gabas, wanda gwamnati ta karyata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Daga ƙarshe, Kotu a jihar Kaduna ta tura shi mai fashin baki a harkokin yau da kullum, Mahadi Shehu gidan gyaran hali.

Kotun ta dauki matakin ne bayan an gurfanar da shi a gaban kotun majistare a ranar Talata 31 ga watan Disambar 2024.

Kotu ta Mahadi Shehu gidan kaso a Kaduna
Kotu ta tunkuda keyar Mahadi Shehu gidan gyaran hali a Kaduna. Hoto: Rescue Nigeria Urgently/Getty.
Asali: Facebook

Musabbabin zargin Mahadi Shehu da ake yi

Kara karanta wannan

An gano dalilin da ya sa 'yan Arewa za su zabi Tinubu a 2027 duk da dokar haraji

The Nation ta ce an gurfanar da Mahadi ne a kan tuhume-tuhume guda biyu: hada baki da tallafa wa ta’addanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan rubutu da Mahadi Shehu ya yi inda ya yi zargin cewa Gwamnatin Tarayya tana shirin kafa sansanin sojin Faransa a Arewa maso Gabas.

Wannan zargi ya danganta da ikirarin shugaban sojin Nijar, Abdourahamane Tchiani.

Sai dai daga bisani gwamnatin Najeriya ta musanta zargin, yayin da binciken gaskiyar labari ya tabbatar da cewa bidiyon da aka wallafa ya dade.

An gano cewa bidiyo na sojojin Najeriya ne a filin jirgin Bamako lokacin aikin ECOWAS a Mali a watan Janairu 2013.

Hukuncin da kotu ta yi kan Mahadi

Abin da Mahdi Shehu ya aikata laifi ne a dokar kasa wanda ya sabawa sashe na 26 (2)(3) na dokar hana ta’addanci ta 2022, da tayar da rikici.

Alkalin kotun, Abubakar Lamido, ya umarci a tura Mahadi Shehu gidan gyaran hali har zuwa ranar 14 ga watan Janairun 2025, domin ci gaba da sauraron shari'ar.

Kara karanta wannan

Tchiani: An samu bayanai daga kasar waje kan zargin Najeriya da hada kai da Faransa

Mahadi Shehu ya caccaki manyan Arewa

Kun ji cewa mai sharhi kan harkokin gwamnati a Arewa ya caccaki yadda shugabannin yankin ke gudanar da mulki.

Mahdi Shehu ya fusata, ya yi zargin cewa gwamnonin ba su da wata sahihiyar hanyar samar da cigaba mai dorewa.

Ya kuma caccaki mutanen Arewa da ke karbar kudi kalilan su na sayar da kuri'arsu a duk lokutan zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.