Ribadu Ya Gano Hanya 1 Ta Dakile Matsalar Tsaro, Ya Fadi Lokacin da Komai Zai Daidaita

Ribadu Ya Gano Hanya 1 Ta Dakile Matsalar Tsaro, Ya Fadi Lokacin da Komai Zai Daidaita

  • Mai ba Bola Tinubu shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu fadi matakan da ya kamata a dauka kan rashin da tsaro
  • Ribadu ya ce yaki da ta'addanci ba zai yi nasara ba sai da hadin kan al'umma da gaggawar bayar da rahoto kan duk abin da ya dace
  • Ya tabbatar da himma daga hukumomin tsaro don samar da tsaro ta hanyar dabaru na zamani da hadin gwiwa a shekarar 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan matsalar tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya kawo mafita kan dakile matsalar tsaro..

Ribadu ya bayyana cewa ba za a iya samun nasara a yaki da ta'addanci da laifukan aikata barna ba sai da hadin kan jama'a.

Ribadu ya bukaci hadin kan al'umma kan matsalolin tsaro
Nuhu Ribadu ya fadi shirin Gwamnatin Tarayya na kawo karshen rashin tsaro. Hoto: Nuhu Ribadu.
Asali: Twitter

Ribadu ya nemi taimakon al'umma kan tsaro

Kara karanta wannan

An kama 'yan fashi 189, masu garkuwa 39 da 'yan daba 1,987 a Kano

Ribadu ya bayyana haka ne a cikin sakon sabuwar shekara ta hannun Manajan Cibiyar Yaki da Ta’addanci ta Kasa, Manjo Janar Adamu Laka a cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban EFCC ya ce hakki ne a kan kowa domin ba da rahotanni saboda dakile matsalolin tsaro.

“Tsaro hakkin kowa ne, ina kira ga kowa da kowa ya gaggauta bayar da rahoto kan duk wani abu da ake zargi ga hukumomin tsaro.”
"Hadin kan sojoji, hukumomin tsaro, da goyon bayan jama’a zai tabbatar da samun nasara a kan kalubalen tsaro.”

- Nuhu Ribadu

Ribadu ya yabawa dakarun sojojin Najeriya

Ribadu ya gode wa dakarun soji, ‘yan sanda, da sauran jami’an tsaro da suka taka rawar gani a shekarar da ta gabata wajen samar da tsaro a kasa.

Ya tabbatar da cewa a shekarar 2025 za a magance ta’addanci, tsattsauran ra’ayi, da sauran manyan laifuka ta hanyar hadin kai da dabarun zamani, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

"Wahalarku ba za ta tafi a banza ba," Tinubu ya aika sakon 2025 ga 'yan Najeriya

Ya kara da cewa an samar da wuraren aiki da suka hada hukumomi da dama don yaki da garkuwa da mutane tare da goyon bayan Hukumar Laifuka ta Birtaniya.

Ribadu ya mayar wa Tchiani martani

Kun ji cewa Gwamnatin Najeriya ta musanta zargin da Nijar ta yi na cewa ana hada baki da ita wajen kokarin jefa hargitsi kasar.

Hakan ya biyo bayan zargin shugaban Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya yi na cewa Najeriya na cutar da kasarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.