Kotu Ta Amince a Tsare Shugabannin Miyetti Allah na Kwanaki 60

Kotu Ta Amince a Tsare Shugabannin Miyetti Allah na Kwanaki 60

  • Shugaban kungiyar Miyetti Allah, Bello Bodejo zai ci gaba da zama a hannun hukumomin tsaron kasar nan
  • Wannan ya biyo bayan hukuncin da alkalin babbar kotun tarayya, Mai Shari'a Emeka Nwite ya yanke kan bukatar DIA
  • Hukumar leken asirin sojin kasar nan ta shigar da Bodejo kara bisa zargin ta'addanci da kai wa sojoji hari a Nasarawa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Babbar kotun tarayya a Abuja ta amince da bukatar da Hukumar leken asiri ta soji (DIA) ta shigar a kan shugaban Miyetti Allah, Bello Bodejo. Kotu ta ba wa hukumar DIA damar ci gaba da tsare Alhaji Bello Bodejo, shugaban Miyetti Allah Kautal Hore, da wasu mutum shida har na tsawon kwanaki 60.

Kara karanta wannan

"Wuce gona da iri," Dattawan Arewa sun ce a biya diyyar wadanda sojoji suka hallaka a Sakkwato

Bodejo
Kotu ta amince a ci gaba da tsare Bello Bodejo Hoto: HQ Nigerian Army/Bello Bodejo
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito Mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da wannan umarni bayan sauraron bukatar gaggawa da lauya na DIA ya gabatar.

'Yan kungiyar Miyetti Allah da DIA ke kara

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa DIA ta shigar da karar Bello Bodejo, Suleiman Abba, Umar Jibrin da Umar Bello.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran mutanen da DIA ke son tsare wa su ne Muhammed Ayuba, Jibrin Baba, da Saidu Wakili, a matsayin wadanda ake kara na daya zuwa na bakwai.

Dalilin kai 'yan Miyetti Allah kotu

Bonny Ozegbe, jami’in bincike na DIA, ya bayyana cewa sojojin Najeriya ne suka kama wadanda ake kara a Nasarawa a ranar 11 ga Disamba sannan suka mika su ga DIA don ci gaba da bincike.

Ozegbe ya yi ikirarin cewa an kama wadanda ake kara saboda zargin ta’addanci da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, sannan ana zarginsu da ta'addanci da hannu a harin a kan sojoji.

Kara karanta wannan

Rashin nadamar cire tallafin fetur da abubuwa 3 da Tinubu ya fada a kan manufofinsa

Miyetti Allah: Kotu ta amince da bukatar DIA

A yayin yanke hukunci, mai shari’a Nwite ya ce bayan sauraron jawabin Odom, ya gano cewa bukatar da aka shigar tana da muhimmanci.

Ya ce:

“An amince da bukatar."

Mai shari’a Nwite ya dage ci gaban shari’ar zuwa ranar 3 ga Maris, 2025, don ci gaba da sauraron kara.

Majalisa ta nemi a saki shugaban Miyetti Allah

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar wakilan Najeriya ta fusata da tsare shugaban Miyetti Allah, Bello Bodejo ba bisa ka'ida ba da sojojin kasar nan suka yi.

Ana zargin cewa Bataliya ta 177 ta Sojin Najeriya ne ta saka aka kama Bello Badejo saboda wata hatsaniya da ta faru a kwanakin baya, lamarin da ya sa aka ci gaba da tsare shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.