An Kama 'Yan Fashi 189, Masu Garkuwa 39 da 'Yan Daba 1,987 a Kano
- Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da manyan nasarorin da ta samu wajen yaki da laifuffuka a shekarar 2024
- Kwamishinan 'yan sanda, CP Salman Dogo Garba ya yi bayani kan tsare-tsaren inganta tsaro a jihar a shekarar 2025
- Rahotanni sun nuna cewa rundunar ta kama mutum 2,425 da ake zargi da laifuffuka, tare da kwato muggan makamai da dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan Kano ta gabatar da jawabin shekara kan nasarorin da ta cimma wajen tabbatar da tsaro a 2024.
CP Salman Dogo Garba ya bayyana cewa nasarorin da suka samu sun kai ga rage aikata manyan laifuffuka a jihar.
Kakakin 'yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya wallafa jawabin CP Salman Dogo a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Laifuffukan da aka yaka a Kano a 2024
CP Salman Dogo Garba ya ce an tsara ayyuka yaki da laifuffuka ne ne bisa umarnin Sufeton ‘Yan Sanda na kasa, IGP Kayode Egbetokun.
Tsare-tsaren sun hada da yaki da ‘yan daba, fashi, satar shanu, da shawo kan rikicin manoma da makiyaya.
Ya bayyana cewa dabarun da suka bi sun hada da amfani da bayanan sirri, aiki tare da hukumomi, da kuma fadakar da jama’a kan mahimmancin tsaro.
Nasarorin da 'yan sanda suka samu a 2024
Punch ta wallafa cewa rundunar ta kama mutane 2,425 da ake zargi da aikata manyan laifuffuka a Kano cikin 2024.
Jerin adadin mutanen da aka kama da laifuffuka daban-daban:
1. 'Yan fashi - 189
2. Masu garkuwa da mutane - 34
3. Barayin shanu - 10
4. Masu safarar bindigogi - 2
5. Barayin mota - 22
6. Masu safarar miyagun kwayoyi - 58
7. Masu safarar mutane - 18
8. Masu satar Neke napep - 46
9. Masu satar babura - 28
10. Masu buga jabun takardun kudi - 4
11. 'Yan damfara - 27
12. 'Yan daba - 1,987
Haka zalika, an kwato bindigogi 24, alburusai 1,213, motoci 12, keke napep 15, da kuma jabun kudi da suka kai sama da Naira biliyan 129.
Shirin 'yan sanda a shekarar 2025
CP Salman Dogo ya ce za su kara kaimi wajen aiwatar da tsare-tsaren da suka samar da nasarori a bana.
Rundunar za ta ci gaba da tsaurara yaki da laifuffuka da kuma yin amfani da dabarun zamani wajen tabbatar da tsaro.
Kwamishinan ya yaba wa gwamnatin jihar Kano, ‘yan jarida, da al’ummar jihar kan hadin kan da suka bayar wajen samun nasarorin da aka cimma.
2024: An kama 'yan bindiga 40 a Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta fitar da rahoton karshen shekara kan nasarorin da ta samu a 2024.
Kwamishinan 'yan sandan jihar ya bayyana cewa sun samu nasarar kama 'yan bindiga masu garkuwa da mutane 40 da sauran miyagu da dama.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng