Halilu Sububu da Wasu Hatsabiban Shugabannin 'Yan Bindiga 16 da Aka Kashe a 2024

Halilu Sububu da Wasu Hatsabiban Shugabannin 'Yan Bindiga 16 da Aka Kashe a 2024

  • Aƙalla shugabannin 'yan ta’adda 17 sun gamu da ajalinsu a karkashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2024
  • Sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta’adda 10,937, ciki har da fiye da shugabannin 'yan bindiga 1,000, tare da ceto mutane 7,063
  • Ranar Talata, 31 ga Disamba, 2024, hedkwatar tsaro ta bayyana shugaban 'yan ta’adda Bello Turji da cewa "gawa ta ki rami" ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Rundunar sojin Najeriya ta bayyana shugaban 'yan ta’adda Bello Turji, a matsayin "gawa ta ki rami" a ranar Talata, 31 ga Disamba.

An rahoto cewa Bello Turji, shugaban 'yan bindiga ne kuma dan ta'adda da ya shahara a Arewa maso Yamma, musamman a jihohin Sokoto, Zamfara, da Neja.

Sojoji sun jaddada kudurin gwamnatin Bola Tinubu na kawo karshen ta'addanci a Najeriya
Akalla hatsabiban shugabannin 'yan ta'adda 17 ne sojoji suka kashe a shekarar 2024. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

An halaka 'yan ta’adda da dama a 2024

Kara karanta wannan

DHQ ta fadi adadin shugabannin 'yan ta'addan da sojoji suka kashe a 2024

Edward Buba, daraktan yada labarai na hedikwatar tsaro, ya bayyana cewa rundunar sojin Najeriya ta kashe shugabannin 'yan ta'adda da dama a cikin shekarar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Cable ta ruwaito Buba yana cewa:

"Domin waiwayen baya, zan bayyana wasu sunayen manyan shugabannin 'yan ta'adda da muka kashe tun farkon wannan shekara."

Ya kara da cewa:

"Wadannan sun hada da: Halilu Sububu, Dutse Mainasara Idda, Mallam Saleh Umaru, Mohammed Amadu, Abubakar Musa, Adamu Tanko Ibrahim, Yellow Dogon Rakumi, Isiya Boderi, da Alhaji Baldu."

Manjo Janar Buba ya ci gaba da cewa:

"Sauran sun hada da Usman Modi Modi, Kachalla Halilu, Kachalla Tukur, Amir Ibrahim Bukar, Saidu Hassan Yellow, Buba Kachalla Bukar, Bakura Jega, da Abba Tukur."

Jerin shugabannin 'yan ta’adda 17 da aka kashe:

  1. Halilu ‘Buzu’ Sububu
  2. Dutse Mainasara Idda
  3. Mallam Saleh Umaru
  4. Mohammed Amadu
  5. Abubakar Musa
  6. Adamu Tanko Ibrahim
  7. Yellow Dogon Rakumi
  8. Isiya Boderi
  9. Alhaji Baldu
  10. Usman Modi Modi
  11. Kachalla Halilu
  12. Kachalla Tukur
  13. Amir Ibrahim Bukar
  14. Saidu Hassan Yellow
  15. Buba Kachalla Bukar
  16. Bakura Jega
  17. Abba Tukur

Kara karanta wannan

'Gawa ta ƙi rami': Hedikwatar tsaro ta fadi shirinta na kawo ƙarshen Bello Turji

"Abin da ke jiran Bello Turji" - DHQ

Tun da fari, mun ruwaito cewa hedikwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta ce shugaban 'yan ta'adda Bello Turji ya kusa zama shekakke kamar yadda ta kashe magabatansa.

Manjo Janar Edward Buba ya ce sojoji sun kashe hatsabiban shugabannin 'yan ta'adda da suka yi barazana irinta Bello Turji, don haka shi ma ajalinsa na nan zuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.