Hukumar Hisbah Ta Fara Tsince Yara da ke Gararamba a Titunan Kano
- Shugaban hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce an fara kwashe yara da ke yawo a tituna da kasuwanni
- Ya ce gwamnatin Kano ta dauki matakin ne domin yin riga kafin matsalar tsaro da zamantakewa da za su iya haddasa nan gaba
- An kama yara da su ka fito daga jihohin Arewa daban-daban da makociyar Najeriya, jamhuriyar Nijar da yawansu ya kai 220
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta ce an kammala shirin fara kwashe dubban kananan yara da ke gararamba a titunan jihar.
Shugaban hukumar Hisbah a jihar, Sheikh Aminu Daurawa ne ya tabbatar da fara shiri a ranar Litinin domin dakile barazanar zamantakewa da tsaro.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh Daurawa ya kara da cewa tuni aka fara tsince yaran da ke yawo a kasuwanni da karkashin gadoji.
"Yara 5,000 na gararamba," Gwamnatin Kano
BBC Hausa ta wallafa cewa shugaban hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa akalla yara sama da 5,000 ne ke gararamba a Kano.
Sheikh Daurawa ya kara da cewa;
"Ci gaba da rayuwarsa a waɗannan wurare zai iya haifar da matsala ta tsaro da ta zamantakewa a nan gaba,"
Gwamnatin jihar Kano ta kama yara 220
Hukumar Hisbah ta ce zuwa yanzu, ta kama yara akalla 220 da ke gararamba a titunan Kano, kuma an sauke su a sansani na musamman da aka tanada.
Hukumar ta ce an kamo yaran ne daga kasuwanni da karkashin gadoji da sauran wurare a jihar, inda aka killace su kafin a fara daukar mataki na gaba.
Adadin yaran da aka kama a Kano da jihohinsu
1. Maiduguri 8 2. Kano 86 3. Katsina 44 4. Jigawa 16 5. Gombe 3 6. Jamhuriyar Nijar 11 7. Niger 4 8. Bauchi 7 9. Yobe 6 10. Kaduna 18 11. Kebbi 2 12. Sakkwato 3 13. Nasarawa 1 14. Zamfara 10
Hisbah ta yi sababbin dokoki a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar Hisbah ta fitar da sababbin dokokin hira, inda ta haramta wa maza da mata taɗi a cikin mota mai duhun gilashi bayan karfe 10.00 n.d.
Haka kuma hukumar ta hana mata hawa Keke Napep bayan karfe 10.00 n.d, da barazana ga masu ba da haya ana buga wasan caca, inda ta ce za ta fara cafke masu wannan dabi'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng