"Na Gaji da Rayuwar nan": Ƴar Marigayi Ado Bayero na Barazanar Hallaka Kanta a Bidiyo

"Na Gaji da Rayuwar nan": Ƴar Marigayi Ado Bayero na Barazanar Hallaka Kanta a Bidiyo

  • Zainab Ado Bayero ta bayyana mawuyacin halin da take ciki a Legas tun bayan rasuwar mahaifinta, marigayi sarkin Kano
  • Diyar tsohon sarkin ta ce mahaifinta ya bar ta ba tare da ilimi ko muhalli ba, kuma babu wanda ya damu da halin da take ciki
  • Zainab ta roki gwamnati da sarkin Kano na yanzu amma ta ce ba a dauki mataki ba, tana barazanar kawo karshen rayuwarta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Zainab Ado Bayero, ‘yar marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero, ta bayyana yadda ta ke fama da damuwa bayan rasuwar mahaifinta.

A cikin wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, Zainab Ado ta ce iyalinta suna cikin mawuyacin hali tun bayan rasuwar Srkin.

Zainab Ado Bayero ta yi magana kan mawuyacin halin da suke ciki da mahaifiyarta a Legas
'Yar marigayi Ado Bayero ta fadi mawuyacin halin da take ciki, da barazanar halaka kanta. Hoto: @NigeriaAbc
Asali: Twitter

'Yar tsohon sarkin Kano ta saki sabon bidiyo

Kara karanta wannan

"Jiki duk yunwa," Tsohon shugaban majalisa ya fadi illar barin Arewa talauci

A cikin bidiyon da jaridar The Nation ta wallafa a shafinta na X, Zainab Ado ta bayyana cewa tana cikin Lagos ba tare da tallafi ko kayan more rayuwa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Diyar Ado Bayero ta ce mahaifinta ya rasu ya bar ta ba tare da ya ba ta ilimi ko muhalli ba.

Cikin yanayi mai ta da hankali, diyar tsohon sarkin Kano ta shaida cewa babu wanda ya damu da ta rayu ko ta mutu, shi ya sa babu mai jin kokenta.

Ta yi ikirarin cewa, babu wanda ya amsa bukatunta a koken da ta kaiwa shugaban kasa, sarkin Kano na yanzu, da ma gwamnan jihar.

"Babu wanda ya damu" - Diyar Ado Bayero

A bidiyon, Zainab Ado Bayero ta ce:

"Ina kan titin Lagos, ba mu da wurin zuwa, ba wanda zan iya tuntuba, yanzu haka ina kusa da otel din Eko, babu wani wanda zai taimaka mana."

Kara karanta wannan

"Dalilinmu na daga wa gwamnati kafa," ASUU na shirin tsunduma yajin aiki

"Na kasa ci gaba da wannan rayuwar. Wai a haka ni ‘yar sarkin Kano ce da ke gararamba a titin Lagos, cikin wahala, ba wanda ya damu ko zan rayu ko zan mutu."
"Mahaifina ya rasu ya bar ni ba tare da komai ba; babu gida, babu ilimi, babu aiki. Ina fama da wahala ba tare da samun wani tallafi ba."
"Mahaifiyata da kanina sun dogara da ni, amma yanzu na rasa yadda zan kula da su. Na gaji da wannan rayuwar cikin wahala."

Zainab Ado na barazanar hallaka kanta

Zainab Ado Bayero ta ci gaba da cewa:

"Na yi kokarin rokon gwamnati, shugaban kasa, gwamna, da sarkin Kano na yanzu, amma babu wanda ya damu da halin da nake ciki."
"Na gaji da rayuwar wahala. Ina jin tamkar babu wanda ya damu idan na rayu ko na mutu don haka zan kawo karshen rayuwata saboda ba zan iya ci gaba a haka ba."

Kara karanta wannan

"An samu tsaro a 2024," Gwamnan a Arewa ya yabawa Shugaban Kasa Tinubu

"Ga duk wanda ya ga bidiyon nan, ina so na ba mahaifiyata hakuri da kanina, amma ba zan iya ci gaba ba, ban san kuma me ya rage na yi, karshen abin da zan iya yi kenan."

Kalli bidiyon a kasa:

Zainab Ado ta nemi taimakon Abba, Sanusi II

Tun da fari, mun ruwaito cewa diyar marigayi Sarkin Kano, Zainab Ado Bayero, ta bukaci taimako daga Gwamna Abba Kabir da Muhammadu Sanusi II saboda halin da take ciki.

Zainab ta ce an yi yunkurin korarta tare da mahaifiyarta da kaninta daga gida saboda rashin biyan kudin haya, kuma ta nemi Gwamna Alex Otti ya taimaka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.