Tinubu Ya Shiga Jerin Shugabannin Duniya da Suka Yi Fice a Harkar Rashawa

Tinubu Ya Shiga Jerin Shugabannin Duniya da Suka Yi Fice a Harkar Rashawa

  • Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya shiga rukunin shugabannin duniya da suka kware a cin hanci da rashawa
  • Shugaba Tinubu shi ne ya zo na uku, sai takwaransa na Kenya, Samuel Ruto da ya zo na biyu a jerin shugabannin
  • An samu sakamakon ne bayan binciken da Cibiyar kula da manyan laifuka da cin hanci da rashawa ta duniya ta yi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya shiga jerin shugabannin duniya da suka kware a aikata cin hanci da rashawa a duniya a shekarar 2024.

Tinubu ya samu sabon kambun ne bayan rahoton Cibiyar Kula da Manyan Laifuka da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya (OCCRP).

Kara karanta wannan

"Shugabannin APC sun sace Naira tiriliyan 25?" PDP ta ba Tinubu shawarar abin yi

Tinubu
Tinubu ya shiga jerin shugabanni masu aikata rashawa Hoto: ATPImages/William Samoei Ruto/Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa Cibiyar OCCRP ta saba tattara alkaluma daga 'yan jarida, kwararru da sauran masana masu zaman kansu a kan rashawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya zama na 3 a wajen rashawa

Jaridar The Cable ta wallafa cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya zo na uku a cikin jerin shugabannin duniya da suke tsara wa da aikata rashawa.

Wannan ya na kunshe a cikin rahoton OCCRP da aka fitar a ranar Talata, wanda ya kunshi jerin shugabannin duniya da ake zargi da aikata rashawa.

Tinubu, Ruto sun shiga kundin rashawa

Rahoton OCCRP ya bayyana cewa hambararren shugaban kasar Syria, Bashar Al Assad ne ya zo na daya a masu shirya wa da aikata rashawa a duniya.

Sai shugaban Kenya, William Ruto ya take masa baya a matsayin na biyu da kuri'a 40,000, yayin da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya zo na uku.

Kara karanta wannan

"Wahalarku ba za ta tafi a banza ba," Tinubu ya aika sakon 2025 ga 'yan Najeriya

Obasanjo ya shawarci Tinubu kan rashawa

A baya, mun ruwaito tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya shawarci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a kan hanyar da za a bi wajen kawar da rashawa.

Tsohon shugaban ya bayyana cewa dole sai hukumomi yaki da cin hanci da rashawa sun fara aikinsu daga kan shugabannin kasar, kafin a gangaro kan sauran jama'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.