Rai Baƙon Duniya: Kwamishina Mai ci a Najeriya Ta Riga Mu Gidan Gaskiya
- Gwamnatin Bayelsa ta sanar da rasuwar Kwamishinar Harkokin Mata, Elizabeth Bidei, mamba a majalisar zartarwa
- Sanarwar gwamnatin jihar ta nuna alhini ga iyalan marigayiyar, musamman mijinta, Cif Jackson Bidei da 'ya'yansu
- Gwamnati ta yaba wa sadaukarwar Mrs. Bidei wajen bunkasa rayuwar mata a jihar, tana mai cewa za a ci gaba da tuna kyawawan ayyukanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bayelsa - Gwamnatin jihar Bayelsa ta sanar da rasuwar kwamishinar harkokin mata, Elizabeth Bidei.
Gwamna Douye Diri ya nuna alhini kan rasuwar kwamishinar wacce ta kasance mamba mai muhimmanci a majalisar zartarwa ta jihar.
Kwamishinar mata a jihar Bayelsa ta rasu
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinar yada labarai, Hon. Mrs. Ebiuwou Koku-Obiyai, ta fitar, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin jihar ta mika ta’aziyya ga iyalan mamaciyar, musamman mijinta, Cif Jackson Bidei, da 'ya'yansu.
“Zuciyarmu na tare da iyalan da suka rasa masoyiyarsu, addu’armu ita ce Ubangiji ya ba su karfin hali a wannan mawuyacin lokaci.”
“Addu’o’inmu suna tare da masoyanta a wannan lokacin na bakin ciki.
"A kullum za mu tuna gudummawar rayuwarta da ayyukanta ga jihar Bayelsa da jama’arta.”
- Cewar sanarwar
Gwamnatin Bayelsa ta yi alhinin rashi
Sanarwar ta bayyana cewa za a yi matukar kewar Mrs. Bidei saboda jajircewarta da kokarinta wajen bunkasa rayuwar mata, Sahara Reporters ta ruwaito.
Gwamnan da gwamnatin jihar sun bayyana bakin cikinsu game da wannan rashi, suna mai cewa za su ci gaba da tuna basirarta da sadaukarwarta.
Tsohon kwamishina a Kwara ya rasu
Kun ji cewa tsohon kwamishinan yaɗa labarai a jihar Kwara, Alhaji Abdulrahim Adisa ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 91 a duniya.
Kungiyar ƴan jarida (NUJ) reshen jihar Kwara ta tabbatar da rasuwar a wata sanarwa da ta fitar ta hannun sakatarenta a ranar Alhamis 26 ga watan Disambar 2024.
Gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin tare da addu'ar Allah ya ba shi a gidan Al-Jannah.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng