Yan bindiga Sun Shiga Garin Gwamna, Sun Tafka Barna, Yan Sanda Sun Roki Mutane
- Wasu ‘yan bindiga sun sace shugaban ƙungiyar KUDA, Emmanuel Tor Yaji, a Tsar Mbaduku, ƙaramar hukumar Vandeikya, jihar Benue
- Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Benue, Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa an fara bincike don ceto Yaji
- Rundunar ‘yan sanda ta bukaci bayanai masu amfani da za su taimaka wajen gano inda aka boye Yaji da ceto shi lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Benue - Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi ta'asa a jihar Benue da ke Arewacin Najeriya.
Maharan sun yi garkuwa da shugaban ƙungiyar Kunav (KUDA), Emmanuel Tor Yaji a ranar Litinin 30 ga watan Disambar 2024.
Yan bindiga sun yi barna a Benue
Leadership ta ce lamarin ya faru ne a Tsar Mbaduku, yankin ƙaramar hukumar Vandeikya da ke jihar Benue.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanan da aka tattara sun nuna cewa Tsar Mbaduku shi ne garin gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Benue, Catherine Anene, ta tabbatar da sace Yaji, inda ta ce sun samu rahoton faruwar lamarin kuma sun fara aikin ceto shi.
Yan sanda sun kaddamar da bincike
"A ranar 30 ga Disamba, 2024, da misalin ƙarfe 8:30 na yamma, an ba da rahoton cewa an sace Emmanuel Tor Yaji a Tsar Mbaduku yayin da yake hutawa tare da abokansa."
"Rundunar ‘yan sanda ta tura jami’ai nan take don aikin ceto tare da fara bincike don gano wadanda suka yi wannan danyen aiki."
“Za mu sanar da al’umma yadda aikin ke tafiya yayin da bincike ke cigaba.”
- Catherine Anene
Anene ta yi kira ga jama’a da su bayar da duk wani bayani mai amfani da zai taimaka wajen ceto Yaji.
Tawagar gwamnan Benue ta yi hatsari
A wani labarin, kun ji cewa wani hatsarin mota ya ritsa da tawagar motocin gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia a ranar Lahadi, 29 ga watan Disamban 2024.
Mazauna yankin da lamarin ya auku sun bayyana cewa mutum ɗaya ya rasa ransa sakamakon hatsarin motan da ya auku.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng