2025: An Gano Yadda Filin Saukar Jirgin Tinubu Zai Lakume N4bn Ana Kukan ba Kudi

2025: An Gano Yadda Filin Saukar Jirgin Tinubu Zai Lakume N4bn Ana Kukan ba Kudi

  • Gwamnati za ta kashe Naira biliyan hudu don gina filin saukar jirgin sama mai saukar ungulu na shugaban kasa a Legas
  • Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da kasafin Naira tiriliyan 49.7 domin inganta zaman lafiya, arziki, da ci gaban Najeriya a 2025
  • Gwamnati ta ware Naira biliyan 724 don gina hanyoyi, Naira miliyan 240 don gina makarantu da dai wasu ayyukan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ma’aikatar ayyuka za ta kashe Naira biliyan hudu wajen gina filin saukar jirgi da karamar tashar jirgin ruwa na shugaban kasa a jihar Legas.

Ma’aikatar ayyuka ta tarayyar ta fitar da kudaden wannan aikin cikin kasafin shekarar 2025 da ta tsara kuma majalisar zartarwa ta amince da shi.

Ma'aikatar ayyuka za ta ginawa Tinubu sabon filin saukar jirgi na Naira biliyan 4.
A kasafin kudin 2025, gwamnati ta ware Naira biliyan 4 don ginawa Tinubu filin saukar jirgi. Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Twitter

Matashiya: Tinubu ya gabatar da kasafin 2025

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi zarra, ya gabatar da sama da Naira tiriliyan 1 a kasafin 2025

Legit Hausa ta rahoto cewa a ranar 18 ga Disamba, Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da kasafin Naira tiriliyan 49.7 a gaban majalisar dokoki ta kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya ce wannan kasafin zai karfafa tsarinsa na samar da zaman lafiya, arziki da kyakkyawar makoma ga ci gaban Najeriya.

Bincike kan kasafin ya nuna cewa ma’aikatar ayyuka ta tarayya za ta kashe Naira tiriliyan 1.057 kan ayyukan gine gine da gyare-gyare.

Kudaden da ma'aikatar ayyuka za ta kashe

A kasafin na 2025, ma'aikatar za ta kashe Naira miliyan 240 a gina makarantun gwamnati, Naira biliyan 724 a gina hanyoyi da Naira biliyan 40.6 a sauran ayyukan gine-gine.

A bangaren gyare-gyare, za a kashe Naira miliyan 340 kan makarantu, Naira biliyan 289.4 kan hanyoyi, da Naira biliyan 2.48 kan gine-ginen ofisoshi, inji rahoton The Cable.

Ma’aikatar ta kuma ware Naira biliyan 5 don biyan basussuka, Naira biliyan 5 don biyan kudaden shari’a da Naira miliyan 280 don kula da janareto.

Kara karanta wannan

Majalisa: 'Za a iya samu jinkirin amincewa da kasafin kudin 2025'

Majalisa na iya samun jinkiri kan kasafin 2025

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar dattawa ta ce ba za a amince da kasafin kudin 2025 na N49.7trn da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar a cikin 2024 ba.

Shugaban kwamitin yada labarai, Sanata Yemi Adaramodu, ya bayyana hakan yayin da ake nazarin kasafin a majalisar dokoki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.