Ana Maganar Faransa, Najeriya Ta Nufi Qatar domin Samo Fasahar Tsaro

Ana Maganar Faransa, Najeriya Ta Nufi Qatar domin Samo Fasahar Tsaro

  • Babban Hafsun Sojojin Sama, Hasan Abubakar, ya kai ziyara Doha a Qatar, domin tattaunawa da kamfanin Barzan Holdings kan fasahar tsaro
  • Matakin ya dace da manufar shugaba Tinubu na karfafa dangantaka tsakanin Najeriya da Qatar kan harkokin tsaro da tattalin arziki
  • Tattaunawar ta mayar da hankali kan musayar fasaha da samun hanyoyin zamani domin inganta ayyukan Sojojin Saman Najeriya (NAF)

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Babban Hafsun Sojojin Saman Najeriya, Hasan Abubakar, ya ziyarci birnin Doha na kasar Qatar domin lalubo dabarun bunkasa tsaron kasa.

An ruwaito cewa ziyarar ta kunshi tattaunawa tare da kamfanin tsaro na Barzan Holdings domin samun sababbin dabaru na fasaha.

Najeriya Qatar
Sojojin Najeriya sun ziyarci kamfanin tsaron kasar Qatar. Hoto: Nigeria Air Force HQ
Asali: Facebook

Rundunar sojin saman Najeriya ta wallafa muhimman abubuwan da ziyarar ta mayar da hankali a kai a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Lakurawa: Mazauna Kauyukan Sakkwato suka jawo muka jefa masu bam Inji Sojoji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin zuwan sojojin kasar Qatar

Punch ta wallafa cewa rundunar sojin saman Najeriya ta ce hadin gwiwar NAF da Barzan Holdings zai taimaka wajen samun sababbin fasahohin zamani.

An tabbatar da cewa haɗin gwiwar za ta taimaka wajen cika bukatun aikin sojojin sama ta hanyar samun sababbin kayan aiki masu inganci.

Kamfanin Barzan Holdings na daya daga cikin manyan kamfanonin tsaro na duniya da ke gudanar da bincike da samar da sababbin fasahohin tsaro.

Dangantakar Najeriya da Qatar kan tsaro

Ziyarar Air Marshal Abubakar ta yi daidai da kokarin gwamnatin Tinubu na karfafa dangantaka tsakanin Najeriya da Qatar, musamman kan harkokin tsaro.

Rahotanni sun nuna cewa ziyarar shugaba Tinubu a watan Maris ita ce ta share fagen tattaunawar da ke tsakanin sojojin saman da kamfanin tsaron.

Ana ganin cewa matakin da rundunar sojin ta dauka na daga cikin dabarun tabbatar da ingantaccen tsaro a Najeriya.

Kara karanta wannan

Yaki da yunwa: Gwamna ya gayyato 'yan China domin koyar da noman zamani

Sojojin sama sun kashe 'yan ISWAP

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin saman Najeriya ta samu gagarumar nasara kan 'yan ta'addan ISWAP a wani hari da ta kai musu a jihar Borno.

Yayin farmakin da sojojin suka kai, an hallaka 'yan ISWAP 32, da dama kuma sun jikkata, wanda hakan na cikin hanyar inganta tsaro a Arewa maso Gabas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng