'Gawa Ta Ƙi Rami': Hedikwatar Tsaro Ta Fadi Shirinta na Kawo Ƙarshen Bello Turji

'Gawa Ta Ƙi Rami': Hedikwatar Tsaro Ta Fadi Shirinta na Kawo Ƙarshen Bello Turji

  • Sojoji sun bayyana cewa Bello Turji, wanda ya yi barazanar kai hare hare a garuruwan Zamfara, yana jiran ajalinsa ne kawai
  • Hedikwatar tsaro (DHQ) ta ce sojoji sun kashe fiye da shugabannin 'yan ta'adda 1,000 kuma irin wannan kaddarar ke jiran Bello Turji
  • DHQ ta bukaci 'yan Najeriya da su guji yarda da farfagandar 'yan ta’adda, tana mai nanata shirinta na kawo karshen 'yan bindiga

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hedikwatar tsaro (DHQ) ta bayyana cewa shugaban 'yan ta'adda, Bello Turji, wanda ya yi barazanar kai hari a Zamfara, yana cikin halaka.

Legit Hausa ta rahoto Bello Turji ya bukaci a saki dan uwansa da wasu 'yan ta'adda da sojoji suka kama, in ba haka ba zai kai hare-hare a garuruwan Zamfara.

Manjo Janar Edward Buba ya yi magana kan shirin sojoji na kawar da Bello Turji
Hedikwatar tsaro ta lashi takobin kawo karshen Bello Turji da 'yan bindigar Arewa. Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Facebook

DHQ ta fadi abin da ke jiran Bello Turji

Kara karanta wannan

"Wuce gona da iri," Dattawan Arewa sun ce a biya diyyar wadanda sojoji suka hallaka a Sakkwato

Manjo Janar Edward Buba, kakakin DHQ ya ce sojoji sun kashe fiye da shugabannin 'yan ta'adda 1,000 da magadansu a shekarar 2024, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya tabbatar da cewa irin wannan kaddara tana jiran sauran shugabannin 'yan ta'adda da shi kansa Bello Turji, yana mai cewa "Turji kamar gawa ce ta ki rami".

“Ba za mu bata lokaci wajen shiga gardama da 'yan ta'adda ba. Mun halaka dukkanin wadanda suka yi irin wannan barazanar a baya.”

- A cewar Manjo Janar Buba.

DHQ ta gargadi 'yan kasa kan farfaganda

Ya kara da cewa sojoji sun kashe tare da binne 'yan ta'adda masu yawa a filin daga, ciki har da wadanda suka yi irin barazanar da Bello Turji ya yi.

Ga masu musanta kai farmaki kan sansanonin Lakurawa, Manjo Buba ya ce, gaskiya ce dama ke zama abu na farko da ake rasawa a yakin duniya.

Ya gargadi mutane da su guji amincewa da farfagandar 'yan ta’adda, yana mai cewa wannan yaki ne da Najeriya take yi don tsaron lafiyar 'yan kasar.

Kara karanta wannan

Yadda kauyuka 50 suka watse da Turji ya yi barazana, jigon APC ya shawarci Tinubu

Bello Turji ya kafa sansani a Sokoto

A wani labarin, mun ruwaito cewa Bello Turji, ya kafa sabon sansani a dajin Indaduwa da ke Sokoto inda 'yan ta'addan ke kai hare-hare da toshe hanyar Isa-Marnona.

Majiyoyi sun tabbatar cewa sansanin Indaduwa na da alaka da kai farmaki, garkuwa, da aikata miyagun laifuffuka kan matafiya da mazauna yankin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.