Yadda aka Tattaro Wasu Barayi da 'Yan Bola Jari Masu Sayen Kayan Sata

Yadda aka Tattaro Wasu Barayi da 'Yan Bola Jari Masu Sayen Kayan Sata

  • Rahotanni na nuni da cewa rundunar ‘yan sanda a jihar Ogun ta cafke mutane biyu bisa zargin sata a wurare daban-daban
  • Wadanda ake zargi sun hada da Sadiq Adebayo, wanda aka kama yana cire shingen karfe na gine-gine a wasu gidaje
  • Haka zalika rundunar 'yan sanda ta kama wani matashi mai suna Adekoya Odunowo da aka samu da zargin satar wayoyin lantarki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ogun - Rundunar ‘yan sanda a jihar Ogun ta tabbatar da cafke wasu mutane biyu bisa zargin satar kayayyaki a gidaje.

Kakakin rundunar, SP Omolola Odutola ta tabbatar da lamarin tana mai cewa mutanen sun shiga hannun ‘yan sanda ne bayan samun rahotannin da al’umma suka bayar.

Jihar Ogun
An kama 'yan bola jari a Ogun. Hoto: Legit
Asali: Original

Rahoton Punch ya nuna cewa bayan kammala bincike za a kai wadanda ake zargi gaban kotu domin musu hukunci.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wuta ana shirye shiryen jana'iza, an rasa rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kama barawon karfe a Ogun

Shugaban unguwar Imutu Ayanre, Yekinni Wasiu ya kai rahoto a ranar 29 ga Disamba, 2024, inda ya bayyana cewa wani matashi na tsaka da sata.

Nan take jami’an ‘yan sanda suka nufi wajen suka cafke matashi mai suna Sadiq Adebayo a unguwar yana cire shingen karfe na ginin wani gida.

Bayan bincike, Adebayo ya amsa laifinsa, ya kuma bayyana cewa ya saba satar irin kayan yana sayarwa wani dan bola jari, Abdullahi Sulaimon, wanda aka kama daga baya.

An kama barawon waya da dan bola jari

A daya bangaren, wani mutum mai suna Seun ya tona asirin wani matashi, Adekoya Odunowo wanda aka samu da wani buhu cike da wayoyin lantarki da ake zargin sato su aka yi.

An gano cewa kowace daya cikin wayoyin lantarkin ta kai kimanin N150,000, kuma yana sayar da su ga wani dan bola jari, Rabiu Ismaila, dillalin kaya a Idode, Ago-Iwoye.

Kara karanta wannan

Yadda aka kashe 'yan bindiga 40, aka kama miyagu 916 a jihar Katsina

'Yan sanda sun bayyana cewa dukkansu biyun sun shiga hannun hukuma, tare da kwato kayan da aka sace.

An kai hari wajen zaman makoki a Anambra

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari a wata unguwa ana tsaka da shirye shiryen jana'iza.

Rahoton Legit ya tabbatar da cewa rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa an kashe mutane bakwai ciki har da wasu jami'an tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng