'An Lalata Najeriya Fiye da Kima,' An Tono Wata Tattaunawar Akpabio da Tinubu
- Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce Najeriya na cikin mummunan hali a lokacin da shugaba Bola Tinubu ya karbi mulki
- Sanata Akpabio ya yaba wa matakan gyaran tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta dauka duk da zafinsu ga 'yan Najeriya
- Shugaban majalisar ya fadi yadda suka yi wata tattaunawa da Bola Ahmed Tinubu a kan yadda aka lalata tattalin arzikin Najeriya a baya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Akwa Ibom - Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa Najeriya na cikin mawuyacin hali a lokacin da shugaba Bola Tinubu ya karbi mulki a 2023.
Da yake jawabi a wani taron tallafawa jama’a a Ikot Ekpene, Akpabio ya bayyana matakan tattalin arzikin gwamnatin Tinubu a matsayin matakai masu muhimmanci, duk da cewa suna da radadi.
Rahoton Channels Television ya nuna cewa Akpabio ya ce matakan gyaran suna da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya nan gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Halin da Bola Tinubu ya samu Najeriya
Sanata Akpabio ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya karbi kasar da tattalin arzikinta ya durkushe daga gwamnatin da ta gabata.
Ya kara da cewa ya taba yin hira da Tinubu a kan yadda tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya dagula tattalin Najeriya:
“Lokacin da na tambayi Tinubu game da halin tattalin arzikin da ya gada, ya ce mani, ‘Ban taba tunanin lamarin ya kai haka lalacewa ba.’”
Akpabio ya yabi matakan tattalin Tinubu
Shugaban majalisar dattawan ya yaba wa shugaba Tinubu kan gyare-gyaren da suka hada da cire tallafin man fetur da kudirin haraji.
Vanguard ta rahoto cewa Akpabio ya ce sun yi imanin cewa Tinubu zai sake farfado da tattalin Najeriya kamar yadda ya yi a jihar Legas.
Akpabio ya yi rabon kayan tallafi a Akwa Ibom
Akpabio ya yi kira ga wadanda ya rabawa kayan tallafi da su yi amfani da su wajen bunkasa rayuwar iyalansu maimakon su sayar da su.
Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa kayayyakin tallafin za su isa kowane bangare na jihar Akwa Ibom ba tare da samun tangarda ba.
An zargi gwamnan Bauchi da barazana ga Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi martani ga gwamnan jihar Bauchi kan wasu kalamai da ya yi a kan Bola Tinubu.
Fadar shugaban kasa ta bukaci Sanata Bala Mohammed da ya janye kalaman da ya yi a kan cewa za su nunawa Tinubu asalin halinsu a kan kudirin haraji.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng