An Shiga Fargaba da 'Yan Bindiga Suka Kashe Jami'an Tsaro 2 da Wani Ɗan Kasuwa
- 'Yan bindiga sun kashe mutum uku ciki har da jami'an tsaro biyu a garin Ihiala bisa zargin bijirewa dokar zaman gida
- Shugaban karamar hukumar Ihiala da ke jihar Anambra ya yi kira ga maharan da su mika kansu domin su fuskanci hukunci
- Gwamnatin karamar hukumar na kokarin tabbatar da tsaro duk da wannan cikas da aka samu a cewar Hon. Charles Orjiako
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - An shiga tashin hankali a garin Ihiala a ranar Litinin yayin da 'yan bindiga suka kashe mutum uku saboda bijirewa dokar zaman gida.
Sun kashe wani sanannen ɗan kasuwa, wanda ake kira Oluebube, a wurin kamfaninsa yayin da yake sa ido kan aikin kafa tantuna don wani biki.

Asali: Twitter
'Yan bindiga sun kashe mutane uku
Rahoton Vanguard ya nuna cewa maharan sun afka kamfanin tare da bude masa wuta, lamarin da haddasa firgici da arcewar mutane daga wurin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani harin na daban, miyagun sun kashe jami’an tsaro biyu a gaban sakatariyar karamar hukumar Ihiala.
Shugaban karamar hukumar, Charles Orjiako, ya bayyana bakin ciki kan wannan mummunan harin da ya kashe jami’an tsaron su biyu.
Gwamnatin Ihiala za ta kamo maharan
Charles ya ce harin ya jefa mutane a fargaba, yana mai kira ga maharan da su mika kansu ga hukumomi domin su fuskanci sakamakon abin da suka aikata.
Ciyaman din ya tabbatar da cewa gwamnatinsa zata ci gaba da aiki don tabbatar da tsaro duk da wannan cikas, tare da neman ganin an gurfanar da maharan.
Ya kuma yi kira ga mazauna garin su kasance masu lura da tattara bayanai kan duk wani abu mai kama da na rashin tsaro tare da kai rahoto ga hukumomin tsaro.
'Yan bindiga sun sace dan majalisar Anambra
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan bindiga sun sace ɗan majalisar dokokin Anambra, Justice Azuka, a Onitsha, kuma babu labari kan inda yake tun makon jiya.
Rundunar ƴan sandan Anambra ta ce dakarunta sun bazama domin ceto ɗan majalisar da kuma kamo waɗanda suka sace shi yayin da ta ce za ta fitar da karin bayani.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng