Dan Majalisar NNPP Ya Fallasa Yadda ake Lallashinsa don Amincewa da Kudirin Haraji
- Ɗan majalisar wakilai daga Kano, Dr. Mustapha Ghali ya ce ana son ya shawo kan takwarorinsa a kan ƙudirin haraji
- Ya ce wani ƙusa a Kudancin ƙasar nan da ke majalisar ya nemi ya zo a haɗe don amincewa da kudirin harajin Bola Tinubu
- Amma ya na ganin akwai wasu matsaloli da za su sa amincewa da ƙudurin ya zama babbar matsala ga Najeriya a yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Ɗan Majalisa mai wakiltar Gaya, Ajingi da Albasu a Majalisar wakilai, Dr. Mustapha Ghali, ya bayyana yadda wani takwaransa ya roƙe shi ya mara wa kudirin harajin Tinubu baya.
Dr. Ghali ya ce ɗan majalisar da ya same shi ya na da ƙarfin faɗa a ji a Kudancin ƙasar nan, kuma ya kawo masa zancen ne saboda a cewarsu, Kano ba za ta samu wata matsala da ƙudirin ba.
Daily Trust ta ruwaito cewa ɗan majalisar NNPP ya faɗi haka ne yayin da yake magana da manema labarai a Kano, inda ya mayar da martanin cewa ya fi kusanci da Arewa a kan Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin ɗan majalisa na adawa da ƙudirin haraji
Jaridar The Guardian ta wallafa cewa Ɗan majalisar Kano na ganin sauran ƙasashe da suka aiwatar da sauyin haraji, gwamnati ta samar da yanayi mai kyau.
Amma ya ce ce akasin haka ne abin yake a Najeriya, inda ya ce Ya kuma bayyana cewa ƙasar nan ba ta kai matakin aiwatar da kudirin sauya tsarin haraji a halin da ake ciki ba.
"A yi watsi da ƙudirin haraji," Ɗan majalisa
Ɗan majalisar NNPP, Dr. Mustapha Ghali ya yi zargin akwai wani shiri a ƙasa game da ƙudirin haraji, saboda haka ya nemi haɗin kan ƴan majaisar Arewa.
Ya ce;
“Abin da zai fi kyau shi ne, dukkan 'yan majalisar Arewa su haɗu kuma su yi aiki domin dakile wannan batu."
“Muna da muradun mutanenmu da muke wakilta. Bai kamata buƙatarmu ta ci karo da muradun wani yanki ba. Wannan shi ya sa muke kira ga mutane su daina yakar junansu don bambancin siyasa, sai dai don samun nasarar yankinmu.”
Kudirin haraji ya fusata ɗan majalisar NNPP
A baya, kun ji cewa ɗan majalisa Kano mai wakiltar Gaya/Abinci/Albasu ya bayyana rashin jin daɗi a kan rahoton da aka fitar ana nuna cewa su na goyon bayan ƙudirin haraji.
Dr. Ghali ya ce wannan ba dai-dai ba ne, saboda haka akwai buƙatar Mataimakin shugaban majalisa, Benjamin Kalu ya gaggauta ajiye kujerarsa domin binciken 'karyar' da ya yi ga jaridu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng