Tinubu Ya Tabo Batun Gyaran Matatar Kaduna bayan Fara Aikin Ta Warri
- Fara aikin matatar Warri da ke jihar Delta a ranar Litinin ya faranta ran shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
- Shugaba Tinubu ya nuna farin cikinsa da dawo aiki da matatar ta yi, ya yabawa kamfanin NNPCL bisa wannan gagarumar nasarar
- Mai girma Bola Tinubu ya kuma buƙaci kamfanin NNPCL da ya ƙara zama wajen gyara matatar Kaduna da ke Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan fara aikin da matatar Warri ta yi a ranar Litinin.
Shugaba Tinubu ya nuna farin cikinsa sakamakon dawowa aikin da matatar ta yi bayan an kwashe dogon lokaci ana gyaranta.
Tinubu ya yi murnar dawowa aikin matatar Warri
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a saƙon da ya sanya a shafinsa na X a ranar Litinin, 30 ga watan Disamban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ƙasan ya bayyana cewa fara aikin matatar abin farin ciki ne a gare sa da ƴan Najeriya baki ɗaya.
Tinubu ya ce dawo da aikin da matatar ta yi zai ƙara ƙarfin gwiwar ƴan Najeriya kan alƙawarin da gwamnatinsa ta yi na samar da gobe mai kyau ga ƙasar nan.
"Ina kuma farin ciki cewa kamfanin NNPCL yana aiwatar da umarnin da na bayar da dawo da dukkanin matatunmu guda huɗu su koma suna yin aiki yadda ya dace."
"Ina taya murna ga Mele Kyari da tawagarsa a NNPCL bisa yin aiki tuƙuru wajen dawo da abin alfaharin ƙasarmu, da mayar da Najeriya cibiyar tace ɗanyen man fetur a Afirika."
- Bola Tinubu
Shugaba Tinubu ya tuna da matatar Kaduna
Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci kamfanin NNPCL ya ƙara azama wajen aikin gyara matatar Kaduna da sabuwar matatar Port Harcourt.
Ya ce hakan zai ƙara tabbatar da matsayin Najeriya wajen samar da makamashi a duniya.
Tinubu ya amince a kafa jami'a a Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa mai girma Bola Ahmed Tinubu ya amince a kafa sabuwar jami'a a yankin Kudancin Kaduna.
Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima shi ne ya sanar da wanann abin albishir ɗin bayan ya je wata ta'aziyya a yankin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng