Kwastam Ta Kama Bindigogi 844, Ta Tara Naira Tiriliyan 5.1 na Kudin Shiga a 2024
- Shugaban Kwastam, Adewale Adeniyi, ya ce hukumar ta kama bindigu 844 da harsasai 112,500 ta hanyar bincike a Tashar Onne
- Hukumar Kwastam ta samu Naira tiriliyan 5.1 a 2024 ta hanyar amfani da fasaha da karfafa biyayya ga dokokin tattara haraji
- Adeniyi ya yi bayanin yadda hukumar Kwastam ta zage damtse wajen ganin ta kare iyakokin kasar daga dukkanin barazana
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban hukumar Kwastam ta Najeriya, Adewale Adeniyi, ya ce ta hanyar bincike, NCS ta kama bindigu 844 da harsasai 112,500 a Tashar Onne.
Adewale Adeniyi ya ce ta hanyar amfani da fasahar zamani, hukumar Kwastam ta samu kudaden shiga na Naira tiriliyan 5.1 a shekarar 2024.
Da yake jawabi a taron tsaro na 18 na Afrika a Doha, Adeniyi ya bayyana yadda hukumar Kwastam ke karfafa tsaro da saukaka kasuwanci, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwastam ta nuna tasirin tsaron iyakoki
A jawabin nasa, Adeniyi ya jaddada kokarin da NSC ke yi wajen kula da kan iyakoki wajen tsaron kasa, yana mai cewa iyakoki sun zarce iyakar kasa da kasa kawai.
Shugaban hukumar ta Kwastam ya ce iyakoki muhimman ƙofofi ne da ke alamta ƙarfin kasa wajen kare jama'arta, tattalin arzikinta da kuma samar da tsaro.
Ya kara bayyana cewa, ikon Dokar Kwastam ta 2023 ya ba hukumar damar gyara ayyukanta don magance barazana da bunkasa hadin kai.
Nasarorin da Kwastam ta samu a 2024
Adeniyi ya ce Dokar Kwastam ta 2023 ta sauya hukumar zuwa mataki mafi inganci a duniya duk da tarin kalubalen da take fuskanta.
A karkashin jagorancinsa, Adeniyi ya ce hukumar NCS ta tara kudaden shiga da suka kai Naira tiriliyan 5.1 ta hanyar amfani da fasaha da karfafa biyayya ga dokoki.
Adeniyi ya bayyana yadda aka kama makamai da dama ta hanyar bincike, ciki har da bindigu 844 da harsasai 112,500 a Tashar Onne.
"Wannan matakin ya rage yaduwar makamai kanana da manyan, wanda ke barazana ga tsaron kasa.
- Inji shugaban hukumar NSC.
Kwastam ta fara daukar sababbin ma'aikata
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar Kwastam ta Najeriya ta yi kira ga daukacin 'yan Najeriya da su cike bukatar neman gurbin aiki a NCS.
Hukumar ta ce akwai guraben aiki a rukunoni uku wanda ya ke bukatar masu karatun digiri, HND, ND da kuma matakin karatun sakandare.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng