Cire Tallafi a Najeriya Ya Jawo wa Gwamnati Kabakin Arziki daga Bankin Duniya

Cire Tallafi a Najeriya Ya Jawo wa Gwamnati Kabakin Arziki daga Bankin Duniya

  • Wasu takardun bankin duniya sun nuna yadda aka bai wa gwamnatin Najeriya ba shi a cikin sauri bisa wasu dalilai
  • Daga cikin dalilan da aka gano akwai cire tallafin man fetur da gabatar da kudurorin haraji a gaban majalisar Najeriya
  • Wadannan tsare-tsare da ya samar wa Najeriya irin wannan gwaggwaban rance ya jefa jama'ar kasar a matsin rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Bankin Duniya ya kammala bayar da bashin $1.5bn ga Najeriya, biyo bayan aiwatar da muhimman sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin tarayya ta yi.

Daga cikin waɗannan sauye-sauyen akwai cire tallafin mai da gabatar da cikakkun manufofin haraji, waɗanda da yawa daga cikin ’yan Najeriya suke kuka da su.

Tinubu
Gwamnati ta samu basussuka da dama daga Bankin Duniya Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

A bayanan da jaridar The Punch ta samu, wannan bashi na daga cikin mafi sauri da Najeriya ta taba samu, inda aka saki duka kudaden cikin kasa da watanni shida.

Kara karanta wannan

Rashin nadamar cire tallafin fetur da abubuwa 3 da Tinubu ya fada a kan manufofinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda bankin duniya ya ba Najeriya bashi

A bisa bayanan da aka samu daga takardun Bankin Duniya, an amince da ba gwamnatin Najeriya bashi a ranar 13 ga Yuni, 2024.

An fara bayar da rukunin farko na $750m wanda aka mika wa gwamnati a ranar 2 ga Yuli, 2024, na biyun kuma aka bayar da shi a watan Nuwamba, 2024.

Bankin duniya ya kara wa Najeriya bashin kudi

Daga cikin sharuddan da suka ba da damar sakin rukunin karshe na bashin akwai cire tallafin mai, wanda aka bayyana a matsayin babbar manufa a cikin sauye-sauyen tattalin arziki.

Wannan saurin bayar da bashin ya sha banban da sauran shirye-shiryen bayar da rance na Bankin Duniya ke yi, wadanda yawanci ke fuskantar jinkiri saboda wasu dalilai.

Bankin duniya yaba wa gwamatin Tinubu

A baya kun ji yadda bankin duniya ya yaba da gwamnatin Najeriya a kan manufofin da aka dauka na farfado da tattalin arzikin kasar da ake cewa ya durkushe.

Kara karanta wannan

"Akwai kullin arziki a 2025," Ganduje ya nemi a kara yi wa Tinubu uziri

Mataimakin shugaban bankin, Indermit Gill ya bayar da tabbacin cewa manufofin su na jefa jama'a a cikin mawuyacin hali, amma za su taimaka wajen ci gaban tattalin arziki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.