"Dalilinmu Na Daga wa Gwamnati Kafa," ASUU na Shirin Tsunduma Yajin Aiki
- Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU), ta bayyana rashin din dadi a kan yadda gwamnati ta ki kula ta
- Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana haka yayin da su ke shirin shiga yajin aiki
- Ya ce sun ba gwamnatin Bola Ahmed Tinubu lokaci domin ta yi abin da ya dace wajen magance matsalolinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) ta bayyana dalilin da yasa ba ta fara yajin aiki a fadin kasar ba, duk da barazanar da ta yi tsawon watanni.
Shugaban kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya tabbatar da cewa kungiyar ta yi nufin jinkirta yajin aikin ne don wata manufa ta musamman.
A hira da Farfesa Osodeke ya yi da jaridar Nigerian Tribune, ya bayyana cewa sun dade su na ba gwamnati damar ta yi abin da ya dace, amma ta ki warware matsalolinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Gwamnati ta yi biris da mu,” ASUU
Kungiyar ASUU ta nuna rashin jin daɗinta game da yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kasa daukar matakan da suka dace don magance matsalolin da kungiyar ta gabatar.
Farfesa Osodeke ya ce:
“Amma har yanzu, bayan watanni da dama, gwamnati ba ta yi wani abu mai ma’ana ba kan dukkanin matsalolinmu ba.”
Kungiyar ASUU ta gaji da jiran gwamnati
Farfesa Osodeke ya kara da cewa, ’yan kungiyar ASUU sun gaji da jiran gwamnati, amma shugabannin kungiyar suna ta roƙonsu su kara hakuri domin ba gwamnatin karin lokaci.
“Lokaci ya yi da za mu dauki mataki kan wannan yajin aikin da muka shirya. Za mu fara aiwatar da shi a farkon watan Janairu idan gwamnati ta kasa yin abin da ya dace kafin lokacin.”
"Mun dade mu na bibiyar gwamnati," ASUU
A karin hasken da ya yi wa majiyar Legit a Kano, shugaban kungiyar na shiyyar Arewa Dr Abdulkadir Muhammad Dambazau ya ce sun sake zama domin ba gwamnati dama.
Dr. Abdulkadir Dambazau ya kuma ce amma dazarar an shiga sabuwar shekara, kuma gwamnatin ba ta yi wani hubbasa ba za su dauki matakin da ya kamata.
Dr. Dambazau ya ce;
"ASUU ta na tafiya yajin aiki ne ba don bukatar kashin kai ba, sai don son ci gaban ilimi."
Gwamnatin Legas ta fusata ASUU
A baya mun ruwaito cewa kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) ta fara yajin aiki a Legas biyo bayan gazawar gwamnatin Babajide Sanwo Olu na biyan sabon tsarin albashi.
ASUU ta ne neman gwamnati ta gaggauta duba kokensu, tare da sake nazarin bambancin albashi da ke tsakanin manyan makarantun jihar da zummar kawo gyaran da ya dace.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng