An Kara Karya Farashin Fetur, Za a Sayar da Litar Mai a N400
- Hukumar Kwastam ta Najeriya ta sanar da shirin sayar da litar fetur guda 15,325 da aka kama a kan farashi mai rahusa
- Rahotanni sun nuna cewa Kwastam ta ce an kama fetur din ne a lokacin samamen da aka gudanar a jihohin Legas da Ogun
- Kwastam ta bayyana cewa hakan na daga cikin matakan rage wahalar sufuri a lokacin bukukuwan karshen shekara
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos - Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta sanar da cewa za ta fara sayar da fetur din da jami’anta suka kama domin rage wahalar sufuri yayin bukukuwan karshen shekara.
Shugaban Operation Whirlwind na hukumar, Hussein Ejibunu ne ya bayyana haka a lokacin taron manema labarai da aka gudanar a Kwalejin Horar da Kwastam da ke Ikeja a Legas.
Legit tattaro bayanai kan yadda kwastam za ta karya farashin fetur din ne a cikin wani sako da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar ta tabbatar da cikar duk wasu sharuɗan doka kafin fara sayar da man fetur din, ciki har da samun umarni daga kotu.
An kama fetur da darajarsa ta kai N27.5m
Hussein Ejibunu ya bayyana cewa, jami’an hukumar sun kama fetur da ya kai darajar Naira miliyan 27.5 yayin samamen da suka gudanar a jihohin Legas da Ogun.
Vanguard ta wallafa cewa Hussein Ejibunu ya tabbatar da cewa na fara aikin ne tun ranar 27 ga watan Mayu na shekarar 2024 kuma an samu nasara sosai.
A cewarsa,
“Babban Kwanturola na Kwastam, Adewale Adeniyi, ya bada umarnin a ci gaba da wannan aiki har sai an dakile ayyukan masu laifi da ke cutar da tattalin arzikin kasar nan.”
Za a sayar da litar man fetur a N400
Hukumar Kwastam ta sanar da cewa za ta sayar da kowace jarka mai daukar lita 25 a kan N10,000, inda kowace lita za ta kama a N400.
Kwastam ta ce mataki na daga cikin shirye-shiryen rage wahalar sufuri yayin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
"Babban Kwanturola ya amince a sayar da fetur din da aka kama ga jama’a domin saukaka matsalar sufuri a wannan lokaci na bukukuwan karshen shekara."
- Hussein Ejibunu
Matatar Dangote ta rage kudin fetur
A wani rahoton, kun ji cewa matatar Alhaji Aliko Dangote da ke jihar Legas ta sanar da rage farashin man fetur ga 'yan Najeriya.
Rahoton Legit ya nuna cewa matatar ta dauki matakin ne domin kawo sauki ga 'yan Najeriya a kan wahalar rayuwa yayin bukukuwan karshen shekara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng