Kwankwaso Ya Gano Bakin Zaren, Ya Fadi Manufar 'Yan Abba Tsaya da Kafarka

Kwankwaso Ya Gano Bakin Zaren, Ya Fadi Manufar 'Yan Abba Tsaya da Kafarka

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ya yi magana kan masu neman Abba Kabir Yusuf ya tsaya da ƙafarsa
  • Sanata Kwankwaso ya nuna cewa masu neman hakan akwai wata manufa ta siyasa da suke son ganin sun cimmawa
  • Madugun na Kwankwasiyya ya kuma musanta zargin da ake yi masa na cewa yana hana ruwa gudu a gwamnatin Abba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya taɓo batun masu cewa Abba Kabir Yusuf ya tsaya da ƙafarsa.

Rabiu Kwankwaso ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda wasu ke ƙoƙarin ganin sun haifar da saɓani tsakaninsa da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf.

Kwankwaso ya yi martani kan Abba tsaya da kafarka
Kwankwaso ya fadi manufar 'yan Abba tsaya da kafarka Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da sashen Hausa na RFI.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi ya shirya liyafa ga abokansa da suka yi yarinta a firamare

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya faɗi manufar ƴan Abba tsaya da ƙafarka

Madugun na Kwankwasiyya ya bayyana cewa masu neman Gwamna Abba ya tsaya da ƙafarsa suna da wata manufa ta siyasa da suke son cimmawa.

Ya ce masu wannan buri na ganin cewa idan suka raba shi da Gwamna Abba, za su iya cimma manufar da suke da ita.

"Wasu tunanin gani suke idan ya tsaya da ƙafarsa ya bar Kwankwasiyya, ba mamaki akwai masu neman gwamna a cikinsu, so suke idan ya yi kuskure sai su haɗa da mu da shi gaba ɗaya su cimma manufarsu."
"Domin haka ina so na godewa shi gwamna, dama da shi suke, to ya fito ya ce ahir."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Kwankwaso ya musanta yin katsalandan ga Abba

Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa zargin da ake jifarsa da shi na cewa yana katsalandan a gwamnatin Abba ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fadi gaskiya kan cimma yarjejeniya tsakaninsa da Atiku, Peter Obi

Ya ce dama tun farko ya ce shawara kawai zai riƙa bayarwa idan an buƙaci hakan, sannan har yanzu abin da yake yi kenan.

Kwankwaso ya magantu kan haɗaka da Atiku, Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan raɗe-raɗin da ake yi na cewa ya cimma yarjejeniya tsakaninsa da Atiku Abubakar da Peter Obi kan tsarin karɓa-karɓa

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya bayyana cewa ko kaɗan babu irin wannan yarjejeniyar da ya cimma tsakaninsa da ƴan siyasan guda biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng