Majalisa: 'Za a Iya Samu Jinkirin Amincewa da Kasafin Kudin 2025'
- Majalisar dattawan Najeriya ta bayyana cewa wasu dalilai za su iya kawo tsaiko wajen amincewa da kasafin kudi
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin a zaman majalisa na hadin gwiwa a ranar 18 Disamba, 2024
- A lokacin da ya kammala gabatar da kasafin, shugaba Tinubu ya roke su da su gaggauta amincewa da kasafin kudin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Majalisar dattawa ta sanar da ‘yan Najeriya cewa kar su yi tsammanin za a amince da kasafin kudin 2025 da aka riga aka gabatar a gaban majalisun kasar nan.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kudin Naira tiriliyan 49.7 a gaban zaman hadin gwiwa na Majalisar dokoki a ranar 18 ga Disamba,.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Bola Tinubu tare ya yi kira ga ’yan majalisar su gaggauta amincewa kasafin kudin shekarar 2025 don ba gwamnati damar fara aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a samu tsaikon amincewa da kasafin kudi
Politics Nigeria ta ruwaito cewa shugaban kwamitin majalisar dattawa a kan harkokin yada labarai, Sanata Yemi Adaramodu ya ce ba za a amince da kasafin kudi kafin 2025 ba.
Ya kara da bayyana cewa akwai wasu dalilai da su ka jawo tsaikon, duk da kira da shugaban kasa ya yi na fatan a gaggauta amincewa da kasafin don fara gudanar da ayyuka.
Dalilin tsaiko a amincewa da kasafin kudi
Sanata Yemi Adaramodu ya shaida wa manema labarai a a Abuja cewa za a fara ma’aikatun gwamnati su fara kare kasafin kudinsu, da sauran hukumomin gwamnati.
Za a fara wannan zama ne daga ranar 7 Janairu 2024, inda ake sa ran Ministoci da shugabannin hukumomi da ma’aikatun gwamnati za su bayyana a gaban majalisa.
Kwamitocin hadin gwiwa na Majalisar Wakilai da ta Dattawa kan Kasafin Kudi za su gabatar da rahoton karshe na kasafin kudin a ranar 31 ga Janairu.
Majalisa na son rage zurarewar kasafin kudi
A wani labarin, kun ji cewa dan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Hon. Bello El Rufa'i ya bayyana takaicin yadda ake samun maimaicin abubuwan da ma'aikatu ke saye duk shekara.
Ya shaida wa zaman majalisa cewa akwai bukatar a rika sa ido, tare da toshe dukkanin kafar da ake amfani da su wajen zurarewar kudin jama'a ta kasafin shekara-shekara a kasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng