Harin Bam a Sokoto: PDP Ta Jajantawa Iyalai, Ta ba Gwamnati Shawara
- Jam'iyyar PDP ta nuna alhininta kan iftila'in harin bam da aka kai kan fararen hula a jihar Sokoto
- PDP ta jajantawa iyalan waɗanda suka rasu da mutanen da suka samu raunuka a harin wanda aka yi kuskuren kai shi kan fararen hula
- Jam'iyyar ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta tabbatar ta ba da diyya ga iyalan mutanen da suka rasu sakamakon kuskuren da jami'an tsaron suka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jam'iyyar PDP ta yi magana kan harin kuskure da sojoji suka kai kan fararen hula a jihar Sokoto.
Jam'iyyar PDP ta jajantawa al'ummar jihar Sokoto kan mutanen da suka rasu da waɗanda suka jikkata sakamakon harin na kuskure da aka kai a ƙauyukan Gidan Sama da Rumtuwa.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ƙasa na PDP, Debo Ologunagba, ya fitar a shafin X a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me PDP ta ce kan harin bam a Sokoto?
Jam'iyyar PDP ta buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da tabbatar da ba da kariya ga fararen hula a yaƙin da ake da ta'addanci a ƙasar nan.
"Jam’iyyarmu ta tuna da aukuwar irin wannan lamari da ya yi sanadiyyar salwantar rayukan fararen hula a jihar Kaduna a watan Disamba 2023 da Satumba 2024, tare da yin kira da a ɗauki matakan kaucewa aukuwar irin wannan bala’i a nan gaba."
- Debo Ologunagba
PDP ta jajantawa iyalan waɗanda lamarin ya ritsa da su, ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakan da suka dace domin biyan iyalan waɗanda suka mutu diyya, tare da samar da isassar kulawa ga mutanen da suka jikkata.
Yayin da ta ke kira da a ƙara sanin makamar aiki, PDP ta buƙaci sojoji da ka da su yi ƙasa a gwiwa a ƙoƙarin da suke yi na yaƙi da ta'addanci a Najeriya.
Shettima ya ba da haƙuri kan harin Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya nemi afuwa kam bam ɗin da aka jefawa fararen hula a jihar Sokoto.
Kashim Shettima ya jajantawa iyalan mutanen da harin wanda aka yi niyyar kai wa kan ƴan ta'addan Lakurawa ya ritsa da su.
Asali: Legit.ng