Zaben 2027: Atiku, Obi da Jam’iyyun Adawa Sun Fara Shirin Tunbuke Tinubu

Zaben 2027: Atiku, Obi da Jam’iyyun Adawa Sun Fara Shirin Tunbuke Tinubu

  • Jam’iyyun siyasa a a Najeriya na ci gaba da bayyana shirin fara zaben 2027 nan ba da dadewa ba, duk da sauran shekaru
  • Jam’iyyun adawa a kasar na ci gaba da kokarin ganin sun hada kai domin tabbatar da an kwace mulki daga hannun shugaba Tinubu
  • Da yawa daga cikin jiga-jigan siyasar Najeriya na yiwa mulkin Bola Tinubu kallon akwai gyara a ciki, lamarin da ke daukar hankali

Najeriya - A shirin zaben 2027, manyan ‘yan siyasa da jam’iyyun adawa sun fara hada kai don ganin an tunbuke Shugaban Kasa Bola Tinubu daga Mulki a zaben shugaban kasa.

Wannan yunkuri ya samu kwarin gwiwa ne daga nasarorin da jam’iyyun adawa suka samu a Amurka da Ghana kwanan nan a zabukan da aka gudanar na shugaban kasa.

A Amurka, tsohon Shugaban Kasa Donald Trump ya kayar da Mataimakiyar Shugaban Kasa Kamala Harris.

Yadda Atiku da Obi ke shirin kwace mulki a Najeriya
Shirin da su Atiku ke yi don tunbuke Tinubu a 2027 | Hoto: @atiku, @peterobi, @RMKwankwaso
Asali: Facebook

A Ghana kuma, John Mahama ya doke Mataimakin Shugaban Kasa Mahamudu Bawumia, wanda hakan ya sa ‘yan adawa a Najeriya suka fara shirin hada kai don kwace Mulki a hannun APC.

Kara karanta wannan

Gawurtattun ‘yan siyasa 6 da suka bar adawa, suka koma jam’iyyar APC a shekarar 2024

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tattaunawa kan hadin kai da aka fara

An ce Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, Peter Obi na jam’iyyar Labour, da tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai suna shirin kafa sabuwar kungiya nan gaba, rahoton Punch.

Rahotanni sun nuna Obi da Atiku sun gana kwanan nan a Yola, amma makusanta sun musanta batun hada gwiwa da ake suna Shirin yi.

Haka zalika, kananan jam’iyyu kamar ADC da PRP suna duba yiwuwar hadewa. Kungiyoyin SDP da CUPP ma suna goyon bayan samar da gagarumin hadin kai don tunkarar APC.

Matsayar tsohon shugaban kasa Obasanjo

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya fara jagorantar wasu tattaunawa don hada kan jam’iyyun adawa.

Ya gana da jiga-jigai irin su Rabiu Kwankwaso da Donald Duke don tsara yadda za a kwace mulkin Tinubu a zaben 2027.

Salihu Lukman, tsohon darakta a kungiyar Progressives Governors Forum, ya yi kira ga tsofaffin shugabanni su mara wa wannan yunkuri baya.

Kara karanta wannan

Talakawa sun yi tururuwa gidan Tinubu neman tallafi, an caccaki shugaban kasa

Kalubalen da ke gaban ‘yan adawa

Ko da yake shirin tsagin adawa yana ta kara karfi, akwai babban kalubale na samun hadin kai daga bangarori da yawa.

Tarihin siyasar Najeriya ya nuna cewa sau daya kawai jam’iyyar adawa ta kayar da jam’iyya mai mulki, wato a zaben 2015 da Muhammadu Buhari ya karbi mulki.

Bugu da kari, Najeriya na fama da matsalolin tattalin arziki, ciki har da hauhawar farashin kaya da bashin da ake bin kasar mai yawa.

Kakakin PDP, Debo Ologunagba, ya ce idan hukumar zabe INEC ta yi zabe mai adalci, Najeriya na iya samun nasarar siyasa kamar ta Ghana da Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.