Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Fadi Lokacin da Matsalar Tsaro Za Ta Kare, Ya Jero Dalili
- Tsohon Gwamnan Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, ya tabbatar da cewa matsalar tsaro za ta ragu sosai a yankin Arewa maso Yamma a 2025
- Yari ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta tura karin jami'an tsaro da kayan aiki don yakar 'yan ta'adda, musamman a Zamfara.
- Tsohon gwamnan ya bukaci al'umma su ba da hadin kai don ganin gwamnati ta cimma burin samar da zaman lafiya mai dorewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari ya ba da tabbacin kawo karshen matsalar tsaro a Arewacin Najeriya.
Sanata Yari ya ce matsalar tsaro da ta addabi Zamfara da yankin Arewa maso Yamma za ta ragu sosai kafin Oktoban 2025.
Yari ya fadi ƙoƙarin gwamnati kan tsaro
Yari ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai a gidansa na Talata-Mafara a jihar Zamfara, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Yari ya jaddada kokarin Gwamnatin Tarayya wajen magance matsalar, musamman ta hanyar tura karin jami'an tsaro musamman a Zamfara.
“A kwanan nan, sojoji sun sayo wasu kayan aiki kuma sun tura su zuwa Arewa maso Yamma, don ganin an kawo karshen wannan fitina ta 'yan bindiga."
“Me ya sa na ce hakan zai yiwu? domin shugaban kasa a kasafin kudi na bana ya ware babban kaso don tsaro." "
A tarihin kasar nan, ko a lokacin mulkin soja ba a taba ware kudin tsaro mai yawa irin wannan ba."
"Saboda haka, cikin ikon Allah, za a yi amfani da kudin yadda ya kamata don tsaron al'umma.”
- Abdulaziz Yari
Yari ya ba manoma tabbaci kan matsalar tsaro
Sanata Yari ya nuna kwarin gwiwa cewa wadannan matakai za su kawo sauki ga jama'ar Zamfara, musamman manoma da ke fama da matsalar tsaro.
“Cikin ikon Allah, zuwa damina mai zuwa, yawancin manomanmu za su koma gonakinsu ba tare da fargabar hari ba."
Abdulaziz Yari
Sanata Yari ya ba da tallafin abinci
Kun ji cewa Sanata Abdul'aziz Yari ya bayar da tallafin tirelar masara 200 domin a rabawa mabuƙata a lungu da saƙo na jihar Zamfara.
Tsohon gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne da nufin sauke farashin kayan abinci a kasuwa da taimakawa marasa ƙarfi.
Asali: Legit.ng