Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Wuta kan 'Yan Ta'addan ISWAP, Sun Sheke Tsageru Masu Yawa
- Dakarun sojojin saman Najeriya sun yi ruwan wuta kan ƴan ta'addan ISWAP a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas
- Sojojin na rundunar Operation Hadin Kai sun hallaka mayaƙan ƙungiyar ta'addancin har guda 32
- Jami'an tsaron sun kuma yi nasarar lalalata makamai masu yawa tare da sauran kayan aikin da ƴan ta'addan suke amfani da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Dakarun sojojin sama na rundunar Operation Hadin Kai sun ƙaddamar da wani hari kan ƴan ta'addan ISWAP a jihar Borno.
Dakarun sojojin sun kai harin ne ta sama a ranar 25 ga watan Disamban 2024, a yankin Dogon Chikun na jihar Borno.
Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda sojoji suka farmaki ƴan ta'addan ISWAP
Dakarun sojojin sun kai farmakin ne bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin ɓangarorin ISWAP.
Majiyoyi sun bayyana sun bayyana cewa harin ya yi sanadiyyar hallaka aƙalla mayaƙan ISWAP guda 32.
Majiyoyin sun bayyana cewa an kai harin ta sama ne a inda mayaƙan ISWAP suka sake haɗuwa bayan arangama da wani ɓangare da ba sa ga maciji da shi.
Baya ga hallaka ƴan ta'addan, an kuma lalata makamai da dama da wasu muhimman kayan aiki na maharan a harin.
"An tsara wannan farmakin cikin dabara kuma an aiwatar da shi ne domin tarwatsa wurin taruwar ƴan ta'addan tare da rage ƙarfinsu na ci gaba da kai hare-hare."
- Wata majiya
Rundunar sojojin Najeriya ta Operation Hadin Kai a yankin Arewa maso Gabas, na ci gaba da zafafa kai hare-hare kan ƴan ta'addan ISWAP da Boko Haram.
Sojoji sun yi gwaninta
Auwal Muhammad ya shaidawa Legit Hausa cewa dakarun sojojin sun yi koƙari sosai kan nasarar da suka samu kan ƴan ta'addan.
Ya yi musu fatan juriya da ci gaba da nuna jajircewa a yaƙin da suke yi da masu tayar da ƙayar baya.
"Wannan nasara ce mai girma kuma abin a yaba ne. Muna yi musu addu'ar Allah ya ci gaba da ba su nasara kan ƴan ta'adda."
- Auwal Muhammad
Sojoji sun ragargaji ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun kai hare-hare kan sansanonin ƴan ta'adda a jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma.
Dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'adda masu tarin yawa bayan sun kai musu hare-hare ta sama da ƙasa a ƙaramar hukumar Danmusa.
Asali: Legit.ng