‘Ku Yi Adalci’: Sheikh Albany Ya Saba da Al’umma game da Zargin Shugaba Tchiani
- Malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Adam Muhammad Albaniy Gombe ya soki zarge-zargen da Shugaban Nijar, Abdourahamane Tchiani ya yi
- Malamin ya ce Tchini zai iya yin kuskure saboda shi ba mala'ika ba ne ko wani Aannabi da komai ya fada gaskiya ne
- Wannan na zuwa ne bayan Tchiani ya zargi Najeriya da hada baki da Faransa domin kassara kasarsa ta Nijar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Gombe - Sheikh Adam Muhammad Albaniy Gombe ya yi magana kan zargin shugaban Nijar a Najeriya.
Shehin malamin ya saba da mafi yawan al'ummar Arewa kan zarge-zargen Janar Abdourahamane Tchiani.
Sheikh Albaniy ya soki Tchiani kan zarge-zargensa
Shehin Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Albaniy ya ce masu fatan sharri za su yadda da maganar Tchiani kamar shi ba zai yi karya ba inda ya ce duk wanda ya yi kazafi Allah ba zai bar shi ba.
Malamin ya ce Tchiani ba Annabi ba ne ko mala'ika da ba zai yi karya ko kuskure a maganganunsa ba.
"Zargin da shugaban kasa Nijar ya yi cewa shugaban kasa ya karbo kwangilar kawo sojojin Faransa domin wargaza kasarsa."
"Mutane da yawa daga sun ji wannan magana sai su gaskata saboda shugaban kasa ne ya fada, watakila zaka ce yana da hanyoyin samun bayanai."
"Amma sun manta shi ba mala'ika ba ne, ba ma'asumi ba ne ba Annabi ba ne bare a ce duk abin da ya fada gaskiya ne."
- Sheikh Adam Muhammad Albaniy
Sheikh Albaniy ya ba al'umma shawara
Malamin ya ce babu abin da ke kawo hayaniya da rigima irin wannan zarge-zarge inda ya ce fadar shugaban kasa ta bakin Nuhu Ribadu ya karyata wannan rahoto.
Ya ce Ribadu ya ba yan jarida damar zuwa wuraren da ake zargi domin bincike da tabbatar da zargin da Tchiani ya yi.
Sheikh Albaniy ya ce babu abin da ya rage tun da an ba yan jaridu dama su yi bincike wanda daman ba a ba su aiki ba ma ya suka kare.
Rarara ya fadi ra'ayinsa kan zargin Tchiani
Kun ji cewa mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya yi fatali da zarge-zargen da shugabanni Nijar, Abdourahamane Tchiani ke yi kan Najeriya.
Rarara ya ce wadannan zarge-zarge soki-burutsu ne kawai inda ya ce babu wanda ke cin dunduniyar Nijar kamar Tchiani.
Asali: Legit.ng