Sojoji Sun Yi Ram da Mata da Ke Samar da Makamai ga Bello Turji, an Cafke Dan Acaba

Sojoji Sun Yi Ram da Mata da Ke Samar da Makamai ga Bello Turji, an Cafke Dan Acaba

  • Rundunar sojojin 'Operation Fansar Yamma' ta kama wata mata mai shekaru 25 da ake zargin tana safarar bindigogi da alburusai 764 zuwa ga ƴan fashi
  • Kakakin sojoji ya bayyana cewa an kama matar da wani abokin tafiyarta ne a Badarawa, karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara
  • Rahoton sirri ya kai ga cafke su yayin da suke kan hanyarsu daga Kware zuwa Badarawa da makaman da ake zargin za su kai ga Bello Turji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Rundunar sojoji ta yi nasarar cafke wata mata ɗauke da alburusai 764 da bindigogi 6 da ake zargin za ta kai ga Bello Turji.

Rundunar sojojin ta 'Operation Fansar Yamma ta samu' ta cafke matar mai shekaru 25 da abokin harkarta a karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

An farmaki wata maboyar gaggan barayi a Kano, an kwato kayan da suka sace

An cafke mata da ke safarar makamai ga Bello Turji
Dubun wata mata ya cika kan zargin kai makamai sansanin Bello Turji a Zamfara. Hoto: Legit.
Asali: Original

Sojoji sun cafke masu ba Turji makamai

Kakakin rundunar, Laftanar-kanal Abubakar Abdullahi, ya ce an kama matar ne tare da abokin tafiyarta ranar 28 Disamba 2024 a Badarawa, cewar Zagazola Makama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar mai suna Shamsiyya Ahadu ta kware wurin safarar alburusai inda aka cafke ta da wasu layu a jikinta.

Har ila yau, tare da Shamsiyya, an kama wani dan acaba mai suna Ahmed Hussaini wanda ake zargi da safarar makamai.

Zamfara: Yadda sojoji suka cafke matar da abokinta

An tabbatar da cafke su ne bayan rahoton sirri da ya nuna suna safarar makamai daga Kware zuwa Badarawa, inda aka kafa shingen bincike.

Wannan nasarar da sojoji suka samu na daga cikin kokarin rundunar wurin tabbatar da kakkabe miyagu a yankin Arewa maso Yamma.

Bello Turji ya ba hukumomi umarni

A baya, kun ji cewa kasurgumin dan ta'adda, Bello Turji ya fitar da sabon bidiyo inda yake gargadi ga hukumomi a jihar Sokoto bayan cafke yan uwansa.

Kara karanta wannan

Lakurawa: Mazauna Kauyukan Sakkwato suka jawo muka jefa masu bam Inji Sojoji

Dan ta'addan ya bukaci sake musu yan uwansu da ke hannun hukumomi ko kuma a fuskanci hare-hare a 2025 da ke tafe.

Wannan na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun tabbatar cewa an cafke wasu daga cikin mataimakan Bello Turji da ya musanta labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.