Malamin Musulunci Ya Bude ‘Dabarar’ da ke Kunshe cikin Kudirin Haraji
- Sheikh Abubakar Abdussalam Babangwale ya yi magana game da kudirin gyaran haraji da ke majalisar tarayya
- Malamin ya ce neman gaggawan amincewa da kudirin ya sa dole a ji tsoro ko akwai wata nuguwar manufa a boye
- A cewar Malam Babangwale, kundin yana da yawa, ba za a samu lokacin nazarinsa sosai ba idan aka yi garaje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Sheikh Abubakar Abdussalam Babangwale ya gabatar da lacca ta musamman game da kudirin harajin da aka kawo kwanaki.
Abubakar Abdussalam Babangwale ya yi bayani game da tasirin kudirin gyaran haraji idan har majalisar tarayya ta amince da su.

Source: Twitter
Cibiyar Islamic Trust of Nigeria da ke Zariya ta shiya lacca ta musamman da malamin musuluncin ya yi magana a kan kudirin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi wa laccan take da ‘sababbin kudirorin dokokin haraji a mahangar addinin musulunci kamar yadda muka gani a shafin Facebook.
Adalci a kudirin gyaran haraji a Najeriya
Malamin addinin da ke zama a garin Kano ya ba gwamnatin Bola Tinubu shawarar ta zama mai adalci a wajen inganta tattalin arziki.
Idan za a fitita wasu jihohi wajen rabon VAT, malamin makarantar ya ce lallai kudirin ya ci karo da da sashe na 17 kundin tsarin mulki.
Duk da haka, ya ce akwai alherai a kudirin, yake cewa sai an yi hankali saboda gudun kawo tsare-tsaren da za su cutar da bayin Allah.
Baban Gwale yake cewa gwamnati ta ce talaka zai samu sauki, amma a fahimtarsu, idan aka dabbaka tsare-tsaren, za a shiga halin ha’ula’i.
Kira ga gwamnati da ‘yan majalisa
Cikin shawarwarin da ya kawo akwai batun cewa ana bukatar a tantance abin da kudirin ya kunsa kafin tafiya ta yi nisa a majalisa.
Shehin yake cewa ka da ‘yan majalisa su yi gaggawa, su bar masana su yi ko da shekaru ne domin nazarin kudirin gyaran harajin.

Kara karanta wannan
‘Kar ku yarda’: Kwankwaso ya zuga ‘yan majalisar Kano su yaki kudirin harajin Tinubu
Ya soki garajen gwamnati wajen kawo tsare-tsaren da za su cutar da al’umma, ya ce an ga haka wajen cire tallafin kudin waje da mai.
Malamin ya ce hakan ya zama dole musamman ganin halin da Arewa ta ke ciki na talauci.
Karamin ma'aikaci zai biya haraji?
A bayaninsa, ya nuna masu karbar mafi karancin albashi ba su huta da biyan haraji ba domin suna samun fiye da N800, 000 a shekara.
Tun da aka amince da albashin akalla N70, 000, mafi kankantan ma'akaci yana samun N840, 000 a shekara, kenan za a tatsi haraji hannunsa.
Idan gaskiya ne lamarin, wannan ya nuna zancen da ake cewa an yafewa kananan ma’aikata haraji a sabon kudirin sam ba gaskiya ba ne.
Asali: Legit.ng
