Bayan Kwanaki 3 Shettima Ya Yi Magana kan Iftila'in Harin Bam a Sokoto
- Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya yi magana kan harin bam na kuskure da sojoji suka kai kan wasu ƙauyukan jihar Sokoto
- Shettima ya nemi afuwa bisa kuskuren da jami'an tsaron suka yi wanda ya jawo asarar rayukan fararen hula 10
- Mataimakin shugaban ƙasan ya jajantawa iyalan mutanen da harin ya ritsa da su wanda aka kai shi kan ƴan ta'addan Lakurawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya nemi afuwar iyalan mutanen da harin bam ya ritsa da su a ƙaramar hukumar Silame ta jihar Sokoto.
Mutane 10 ne suka mutu a ranar Laraba, 25 ga watan Disamba a lokacin da sojoji suka kai hari a wani sansanin ƴan ta'addan Lakurawa a wasu ƙauyuka biyu na ƙaramar hukumar.

Source: Facebook
Sakon jajen na mataimakin shugaban ƙasan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Stanley Nkwocha ya fitar a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan kwanaki uku, Shettima ya jajantawa iyalan waɗanda harin da sojoji suka kai wa ƴan ƙungiyar ta'addancin Lakurawan bisa kuskure.
Me Shettima ya ce kan iftila'in harin bam a Sokoto?
Ya ce lamarin yana ɗaya daga cikin irin waɗannan lokuta na baƙin ciki da fararen hular da ba su ji ba, ba su gani ba tsautsayi zai faɗa musu a ƙoƙarin da ake na kawar da duk wani nau'in ta'addanci a ƙasar nan.
"Dole ne na ce muna neman afuwa tare da baƙin ciki kan asarar rayukan farar hula da raɗadin da ya biyo baya a wannan lokacin mai matuƙar wahala."
"Ina miƙa saƙon jajena ga gwamnati da al’ummar jihar Sokoto, musamman iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a farmakin haɗin gwiwa tsakanin sojin sama da na ƙasa na rundunar Operation Fansan Yamma domin kawar da ƴan ta'addan Lakurawa a ƙauyukan Gidan Sama da Rumtuwa a ƙaramar hukumar Silame."

Kara karanta wannan
'Yan ta'adda sun fara amfani da jirage marasa matuka, DHQ ta tura sako ga 'yan Najeriya
"A madadin jami'an tsaronmu, ina neman afuwa kan wannan babban rashin da aka yi. Ina buƙatar da a ci gaba da ba gwarazan jami'anmu dukkanin taimakon da suke buƙata wajen ayyukansu domin tabbatar da tsaro a ƙasarmu."
- Kashim Shettima
Shettima ya ba da haƙuri
Shettima ya yi kira da a nuna fahimta tare da goyon bayan jami’an rundunar, inda ya ce suna biyan farashi mai tsoka domin kare rayukan waɗanda lamarin ya ritsa da su.
Ya bayyana nadamarsa kan lamarin, a daidai lokacin da yake neman ƙarin goyon baya ga sojojin.
Gwamna ya yi alhini kan harin bam a Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya yi magana kan jefa bam bisa kuskure da sojoji suka yi kan fararen hula a jihar.
Gwamna Ahmed Aliyu ya nuna takaicinsa kan lamarin inda ya ce ya tuntuɓi hukumomin domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Asali: Legit.ng
