Duk da Korafi da Ake Yi, Malamin Musulunci Ya Fadi Jihohi 2 da Za Su Kafa Kotun Shari'a

Duk da Korafi da Ake Yi, Malamin Musulunci Ya Fadi Jihohi 2 da Za Su Kafa Kotun Shari'a

  • Bidiyon Sheikh Dawood Malaasan ya jawo cece-kuce a jihohin Yarbawa kan shirin kafa kotun shari’ar Musulunci a jihar Oyo
  • Sheikh Dawood ya gargadi masu adawa da kotun shari’a, yana cewa za a dauki matakin da ya dace
  • Shehin ya bayyana shirin kafa kotun shari’a a jihohin Osun bayan na Oyo duk da cece-kuce kan batun

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - Sheikh Dawood Malaasan a Iwo, ya jawo cece-kuce a jihohin Yarbawa kan kafa kotun shari’ar Musulunci a jihar Oyo.

A cikin wani bidiyo, malamin ya kare kafa kotun shari’a a jihar Oyo da zafafan kalamai, yana gargadi ga masu adawa da wannan kuduri.

Ana ƙoƙarin kafa kotunan Shari'ar Musulunci a Osun da Oyo
Malamin Musulunci ya ce sun shirya kafa kotunan Shari'ar Muslunci a Oyo da Osun. Hoto: Seyi Makinde.
Asali: Twitter

Kafa kotun Musulunci ya jawo ka-ce-na-ce

Tribune ta ce a cikin gargadinsa ya ce babu wanda ya isa ya hana kafuwar Shari'ar Musulunci a yankin.

Kara karanta wannan

"An samu tsaro a 2024," Gwamnan a Arewa ya yabawa Shugaban Kasa Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya ce bayan jihar Oyo za su tabbatar da kafa kotunan Musulunci a jihar Osun duk da adawar da ake yi.

“Ku da kuke adawa da kotun shari’a a jihar Oyo, ku sani uwarku ba ta haihu da kyau ba."
"Za ku iya komawa wuraren bautarku na gunki ku yi ra’ayinku, amma idan kuka fito fili kuna adawa, za mu dauki matakin da ya dace, ba za mu yi amfani da shari’a a kan wadanda ba musulmai ba."
"Amma muna amfani da dokar shari’a da ke cikin tsarin mulkin Najeriya, ko Yarbawa sun rabu, za mu nemi dokar shari’a.”

- Sheikh Dawood Malaasan

Jihar da za a kafa kotun Shari'ar

Sheikh Malaasan ya kuma bayyana cewa akwai shirin kafa majalisar shari’a a jihar Osun, yana cewa wannan yunkuri ba zai tsaya ba, ko da yankin Yarbawa ya samu ’yancin kansa.

“Ku jira majalisar shari’a a Osun, tana tafe."

Kara karanta wannan

Rashin nadamar cire tallafin fetur da abubuwa 3 da Tinubu ya fada a kan manufofinsa

- Cewar malamin

Kalaman malamin sun jawo martani iri-iri daga al’umma, inda wasu ke goyon bayansa, wasu kuma na sukarsa.

MURIC ta magantu kan kotun Shari'a

Kun ji cewa Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Musulunci (MURIC) ta soki kalaman gwamnan Oyo, Seyi Makinde kan kotunan Shari'a.

Shugaban kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ya ce gwamnan ya na furuci ne ba tare da ilimi ko kara neman sani kan batun ba .

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.