Nijar: Kungiyar ECOWAS Ta Fito Ta Warware Zargin Kasar Najeriya da Ta’addanci

Nijar: Kungiyar ECOWAS Ta Fito Ta Warware Zargin Kasar Najeriya da Ta’addanci

  • ECOWAS ta yi maza ta fitar da jawabi game da ikirarin da aka ji Janar Abdourahamane Tchiani ya yi kwanan nan
  • Kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ba Najeriya gaskiya a sabaninta da makwabciyarta watau Nijar
  • Mai magana da yawun ECOWAS, Joël Ahofodji ya ce Najeriya ba za ta goyi bayan ta’addanci a cikin Afrika ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Kungiyar ECOWAS ta kasashen Yammacin Afrika ta musanya zargin cewa Najeriya ta na hada-kai da kasar Faransa.

ECOWAS ta gaskata Najeriya bayan shugaban Jamhuriyyar Nijar, Abdourahamane Tchiani ya zargi makwabciyarsa ta ta’ddanci.

ECOWAS
Kungiyar ECOWAS ta yi watsi da zargin Nijar a kan Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

ECOWAS ta karyata shugaban kasar Nijar

A wani jawabi da ECOWAS ta fitar a shafukanta na sadarwa kamar X, ta bayyana cewa wannan zargi bai da wani tushe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jiya kungiyar ta yi magana ne ta bakin mai magana da yawunta, Joël Ahofodji, ya na mai watsi da ikirarin na shugaban Nijar.

Kara karanta wannan

Bayan zargin Najeriya, shugaba Tchiani na shan suka daga yan Nijar, sun ba shi shawara

Joël Ahofodji ya ce babu makama ko madogara a zargin da aka yi wa Najeriya ko wata kasa na hada-kai da kasashen da ke Turai.

Mista Joël Ahofodji ya kara da cewa kungiyar ECOWAS ta na tare da gwamnatin Najeriya wanda Bola Tinubu yake jagoranta.

Jawabin kakakin kungiyar ECOWAS

“ECOWAS ta nuna takaici a game da zargin da ake yi wa Najeriya da sauran kasashenta.
"Kungiyar ta na tare da Najeriya da ‘ya ‘yan ECOWAS a kan zargin cewa su na daurewa ta’addanci gindi.
"A tsawon shekaru, Najeriya ta goyi bayan zaman lafiya da tsaron sauran kasashe har a wajen yammacin nahiyar Afrika."

- ECOWAS

An yi kira ga Nijar da sauran kasashe

Daily Nigerian ta ce nasarorinta ECOWAS da jami’an tsaro suke samu a nahiyar ya nuna kokarin Najeriya wajen tabbatar da tsaro.

An bukaci jama’a su guji jefa zargi ba tare da wasu hujjoji ba, a maimakon haka, an nemi su yi abin da zai wanzar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

'Siyasa ce': An zargi Nijar da neman hada gaba mai tsanani tsakanin yan Arewa da Tinubu

Ahofodji yake cewa a yadda aka san Najeriya, ba za ta goyi bayan wani ta’addanci ba.

Sarakuna sun karyata shugaban kasar Nijar

Rahoto ya zo cewa wasu sarakunan gargajiya da ke Arewacin Najeriya sun magantu game da zargin shugaban Nijar kan gwamnatin kasar.

Sarakunan Sokoto da Kebbi da ke iyaka da Nijar sun musanta zargin Abdourahamane Tchiani cewa an ba dakarun sojojin Faransa mafaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng