‘Kar Ku Yarda’: Kwankwaso Ya Zuga ‘Yan Majalisar Kano Su Yaki Kudirin Harajin Tinubu
- Rabiu Musa Kwankwaso bai tare da gwamnatin tarayya a kan zancen sabon kudirin harajin da aka kawo
- Kwankwaso wanda ya nemi mulkin Najeriya a 2023 ya na so ‘yan jam’iyyar NNPP su yaki kudirin a majalisa
- Tsohon gwamnan Kano ya na cikin masu ganin idan aka kara harajin VAT daga 7.5%, kaya za su kara tsada
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Rabiu Musa Kwankwaso ya sake yin magana game da kudirin gyara haraji da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kawo.
‘Dan takaran shugaban kasar a karkashin jam’iyyar NNPP a zaben 2023 ya na cikin wadanda ba su goyon bayan kudirin gyara harajin.

Asali: Twitter
Rabiu Kwankwaso bai na'am da kudirin haraji
A wani bidiyo da wani Amir Abdullahi Kima ya wallafa a shafin Facebook, an ji Rabiu Musa Kwankwaso yana mai adawa da kudirin.

Kara karanta wannan
Rashin nadamar cire tallafin fetur da abubuwa 3 da Tinubu ya fada a kan manufofinsa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Dan siyasar ya yi kira ga ‘yan majalisar da NNPP take da su a majalisar tarayya da su yi adawa da kudirin domin hana shi ya zama doka.
Sanata Rabiu Kwankwaso wanda ake yi wa kallon masoyin talakawa ya soki shirin kara harajin VAT daga 7.5% zuwa 10% a Najeriya.
'Kaya za su tashi idan aka kara VAT' - Kwankwaso
Tsohon Ministan tsaron yake cewa muddin aka kara harajin, talaka sai kara shiga matsin lamba fiye da wanda ake kuka a halin yanzu.
Duk da gwamnati ta kare kudirin, tsohon gwamnan Kano ya ce amincewa da shi zai jawo karin tsadar kayan masarufi a kasar nan.
A maganar da ya yi, Kwankwaso ya nemi ‘yan majalisar da ke wurin taron a Kano su ji kuma su sanar da wadanda ba su wurin a lokacin.
Sanata Kwankwaso ya ba gwamnati shawara
A maimakon karin haraji, ‘dan siyasar yana so gwamnatin Bola Tinubu ta gyara hanyoyi da abubuwan more rayuwa da ayyukan yi.

Kara karanta wannan
'Ba mulkin soja ake ba,' Gwamna ya yi kalamai masu zafi ga Tinubu kan kudirin haraji
“Ba mu goyi bayan a zubawa talakawan Najeriya sabon haraji ba.”
“Idan ba za su yi wa al’umma ayyukan alheri ba, su yi wa Allah, su yi wa Annabi, su kyale al’umma su cigaba da samun kansu a cikin wannan hali mara dadi.
- Rabiu Musa Kwankwaso
'Dan NNPP ya bada hakuri kan kudirin haraji
A cikin ‘yan jam’iyyar NNPP, an ji labari Hon. Abdulmumin Jibrin ya na goyon bayan kudirin da farko, daga baya sai ya canza matsaya.
Jibrin mai wakiltar Kiru da Bebeji ya nemi afuwar daukacin al’umma, ya nuna cewa babu ta inda za a cuci Arewacin Najeriya a kudirin.
Asali: Legit.ng