Bayan Zargin Najeriya, Shugaba Tchiani na Shan Suka daga Yan Nijar, Sun ba Shi Shawara
- Shugaban Nijar, Abdourahmane Tchiani, ya fuskanci suka daga ‘yan ƙasarsa kan zargin da ya yi wa Najeriya na kulla makirci da sauran ƙasashe
- Tchiani ya yi ikirarin cewa Najeriya ta bai wa sojojin Faransa mafaka kusa da Tafkin Chadi tare da kafa sansanonin horar da ‘yan ta’adda
- 'Yan Nijar sun ce zargin Tchiani ba shi da hujja, suna danganta hakan da gazawarsa bayan wata 17 da ya kifar da Bazoum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Niamey, Nijar - Wasu yan kasar Nijar sun soki Shugaba, Abdourahmane Tchiani, kan zargin Najeriya ta kafa sansanonin soji da taimaka wa Faransa wajen kulla makirci domin durƙusar da ƙasarsa.
Masu amfani da kafafen sada zumunta a Nijar sun soki zargin Tchiani, suna cewa ba shi da wata hujja mai karfi.
An soki Tchiani kan zargin Najeriya
The Nation ta ce wasu sun danganta zargin da gazawar Tchiani wajen cika alkawuran da ya yi bayan kifar da Mohamed Bazoum a juyin mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mai fashin baki, Maidalili Namu ya bayyana cewa shugabancin Tchiani na nuna gazawa, yana zargin shi da yayata ƙiyayya a tsakanin ƙasashe makwabta.
Namu ya ce Tchiani ya gagara shawo kan matsalolin Nijar inda ya fake da zarge-zarge domin kawo cikas a zaman lafiyar ƙasashen.
An ba Tchiani shawara kan matsalolin Nijar
“A cikin wata 17, kuna cikin fadar gwamnati ne kawai, kuna samun bayanai marasa tushe da ke dagula tunaninku.”
“Zargin da Tchiani ke yi wa ƙasashe 20 ya nuna gazawar diflomasiyarsa, yayin da matsalolin ‘yan ƙasa suka wuce haka.”
- Maidalili Namu
Masu sharhi sun ce, maimakon magance matsalolin tsaro da tattalin arziki, Tchiani ya maida hankali kan sukar kasashen waje ba tare da wata hujja ba.
Ana zargin siyasa a maganar Tchiani kan Najeriya
Kun ji cewa Hadimin Bola Tinubu a bangaren sadarwa da hulda da jama'a, Daniel Bwala ya yi magana kan zargin Najeriya da Nijar ke yi.
Bwala ya ce zargin da Shugaba Abdourahamane Tchiani na Jamhuriyar Nijar ya yi kan Najeriya da Faransa yaudara ce mara tushe.
Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su yi watsi da wannan zargi yana mai cewa makirci ne don haddasa rikici da gaba a Arewa.
Asali: Legit.ng