Gombe: Dagaci Ya Fadi Yadda Aka Yi bayan Zarginsa da Sassara Matashi kan Zargin Sata

Gombe: Dagaci Ya Fadi Yadda Aka Yi bayan Zarginsa da Sassara Matashi kan Zargin Sata

  • Ana zargin wani dagaci da sassara matashi kan zargin sata a gidansa a unguwar Kagarawal a jihar Gombe
  • Matashin mai suna Adamu Muhammad ya zargi dagacin da ji masa raunuka wanda yanzu yake kwance a gadon asibiti
  • Sai dai dagacin ya musanta labarin inda ya ce yaron yazo masa sata ne inda suka yi artabu sosai kafin kwace wukar hannunsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - Wani maraya ɗan shekara 15, Adamu Muhammad ya shiga mummunan hali a Kagarawal da ke jihar Gombe, inda aka sassara shi da adda har sau bakwai.

Matashin da ya samu karaya saboda saran ya zargi dagacin Kagarawal ne ya aikata masa wannan ta’asa.

Halin da ake ciki kan zargin dagaci da sassara matashi
Ana cigaba da bincike kan zargin dagaci da sassara matashi kan tuhumar sata. Hoto: Gombe Police Command.
Asali: Facebook

Gombe: Ana zargin dagaci da sassara matashi

Aminiya ta ruwaito cewa matashin ya ce a ranar 5 ga Disambar 2024, dagacin, Alhaji Bello A. Usman, ya sassare shi sannan ya umarci a jefar da shi a bola, bayan ya zarge shi da sata.

Kara karanta wannan

Sakon Buhari ga Gwamna Namadi bayan rashin da ya yi, ya fadi abin da ya kamata ya yi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, abin ya samo asali ne bayan ya yi faɗa da wata ’yar maƙwabta, wanda hakan ya sa ta kai ƙorafi ga ’yan banga.

Adamu ya ce ya ƙi komawa gida saboda tsoron fushin mahaifiyarsa, inda ya zaɓi ya kwana a gindin wata bishiya kusa da gidan dagacin.

“Har dare ya fara, ban samu wajen kwanciya ba, sai na tafi gidan dagaci na kwanta a gindin wata bishiya, a kan da safe zan roƙa a je a ba ta haƙuri."
"Ina kwance da misalin ƙarfe 11 sai dagaci ya fito ya yi mini ihun ɓarawo."

- Adamu Muhammad

Game da zargin sata da aka yi masa, Adamu ya bayyana cewa:

“Gaskiya ni ba ɓarawo ba ne, ban taɓa sata ba, hukuma ma ba a taɓa kama ni ba, shi ya sa da yarinyar ta kai ni wajen ’yan banga na gudu, saboda ban san ya zanyi ba, ni latirisha ne a gareji kusa da Masallacin Idin Sarki.”

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya tona yadda ya samawa 'yan jiharsa ayyukan tarayya masu yawa

- Cewar matashin

Mahaifiyar Adamu, Malama Yelwa Muhammad, ta musanta zargin sata da ake yi masa, tana mai cewa:

“Ƙaddara ce, shi ya sa a garin guje wa fushina ya je gidan Dagaci don ya kwana, da ya yi haƙuri da irin faɗan da zan yi masa da haka bai faru ba.”

- Yelwa Muhammad

Abin da dagacin ya ce kan lamarin

A martanin Dagacin Kagarawal, Alhaji Usman A. Bello, ya musanta zargin cewa ya sassara Adamu.

“Na ji motsin mutum yana ƙoƙarin sace mana sitabileza, sai na fito, yaron ya nemi guduwa inda muka yi artabu da shi, na ƙwace wukar da ke hannunsa, na sare shi sau ɗaya a lokacin."

- Alhaji Usman A. Bello

Ya ce bai da hannu wajen kai shi bola, yana mai cewa wasu ne za su iya yin hakan.

Martanin kakakin yan sanda ga Legit Hausa

Kakakin rundunar yan sanda a Gombe, ASP Buhari Abdullahi ya fadawa wakilin Legit Hausa halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta ya ƙara tsananta, gwamna ya fusata, ya soke naɗin sabon sarki

"Eh ana kan matakin bincike har yanzu saboda an fara a ofishin yan sanda a Gombe."
"Daga bisani kwamishinan yan sanda ya bukaci a mayar da binciken hedikwata domin gano ainihin abin da ya faru."

- ASP Buhari Abdullahi

An rasa rayuka a Gombe

Kun ji cewa ana fargabar rasa rayuka yayin da rahotanni suka tabbatar da rikici tsakanin makiyaya da manoma.

Lamarin ya faru ne a ƙauyukan Powishi da Kalindi da ke karamar hukumar Billiri kamar yadda kakakin rundunar yan sanda, ASP Buhari Abdullahi ya fada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.