"Kudirin Haraji Zama Daram," da Abubuwa 3 da Tinubu Ya Fada a kan Manufofinsa
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kara fusata wasu 'yan kasa bayan hira da ya yi da manema labarai a ranar 23 Disamba, 2024, inda ya yi karin bayani a kan shirin gwamnatinsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya kara jaddada akasarin manufofin da gwamnatinsa ta bijiro da su, duk da kuka da jama'a ke yi da mafi yawan tsare-tsaren.
Legit ta tattaro wasu daga cikin kalaman da Tinubu ya yi a kan shirin gwamnatin tarayya ta fuskokin tattalin arziki, tsaro da sauran al'amuran da su ka shafi kasa.
1. Tinubu ya jaddada kudirin haraji
TRT Afrika ta wallafa cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce babu abin da zai sanya gwamnatinsa janye kudirin haraji da ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mafi yawan mazauna Arewacin kasar nan na ganin kudirin zai jawo babbar matsala ga tattalin arzikin Najeriya, musamman idan aka duba tsarin raba haraji.
Sanata Ali Ndume ya na daga cikin 'yan gaba-gaba daga cikin 'yan majalisa da su ke yi wa kudirin bore, tare da neman hadin kan takwarorinsa a kan batun.
Amma a tattaunawa irinta ta farko da manema labarai bayan ya karbi mulki, Tinubu ya nuna cewa duk surutan da ake yi a kan batun ba zai sa a janye kudirin ba.
2. "Ban yi nadamar cire tallafin fetur ba," Tinubu
Tun a lokacin da ya sha rantsuwar shiga ofis ne shugaban kasa, Tinubu ya ayyana janye farashin man fetur, lamarin da har yanzu ke ci gaba da bakanta wa 'yan kasa.
A tattaunawar da aka yi da shi, Shugaban kasa ya ce ba ya yin da-na-sanin matakin da a dauka da janye tallafin man fetur saboda alfanun hakan.
Jaridar Punch ta wallafa cewa Tinubu ya na ganin hukuncin da gwamnatinsa ta yanke na janye tallafin man fetur zai taimaka kwarai wajen daidaita tattalin arziki.
Sai dai har yanzu 'yan Najeriya ba sa ganin amfanin da shugaban kasar ke cewa za a gani ba, inda wata baiwar Allah a Kano, Dr. Salma Ahmad ke ganin shugaban ya shiga hakkin jama'a.
Dr. Salma ta ce;
"Ni sai na ke ganin tun bayan janye tallafin nan aka shiga wata sabuwar matsala. Na san mutanen da sun dai na girkin rana, sai dai safe da dare.
Ni kai na, daga gida zuwa asibitin da na ke aiki, N150 ne kafin a janye tallafin mai, yanzu sai N500 ko N600 haka ake kai ni kullum. To me mutum ya rage?."
3. Shirin Tinubu a kan noma
Yayin da farashin kayan masarufi a Najeriya ke ci gaba da tashin gwauron zabo, Shugaban ya na ganin kara sayo injinan noma za su taimaka wajen magance yunwa.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta sayo injinan noma akalla 2,000, wanda zai taimaka sosai wajen bunkasa noma, wadatar abinci da saukar farashinsu a kasuwannin kasar nan.
Abdullahi Ali Mai Burodi, shugaban gamayyar kungiyar manoma na reshen jihar Kano ya na ganin akwai abubuwa da dama da manoman kasar nan ke bukata daga gwamnati.
Mai Burodi ya kara da cewa;
Akwai bukatar a kawo karshen rikicin manoma da makiyaya, wanda a kwanakin nan su ka rika samun rikice-rikice a karamar hukumar Kura."
Ya ce haka kuma akwai bukatar gwamnati ta rika tabbatar da cewa ana raba tallafin noma ga ainihin manoman kasar nan domin inganta samar da abinci a kasa.
4. 'Ba zan binciki shugannin tsaro ba," Tinubu
Shugaba Tinubu ya jinjina wa jami'an tsaro da shugabanninsu, inda ya tabbatar da cewa ba zai binciki rundunar tsaro a karkashin tsofaffin gwamnati ba.
Ya bayyana cewa yanzu haka, kokarin da dakarun kasar nan su ka yi ya saukaka matsalar tsaro a Arewa, inda ake iya tafiya a mota a wasu sassan.
Tinubu ya kara da cewa gwamnati za ta samar da makamai da sauran kayan aiki domin kara karfafa yaki da ta'addaanci ke kokarin kassara Najeriya.
Matakin gwamnatin Tinubu a kan hauhawar farashi
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ba ta da kudirin kayyade farashin kayayyaki a kasuwannin da ke fadin Najeriya.
Shugaban, wanda ya bayyana haka yayin tattaunawa da manema labarai a Legas, ya kara da cewa amma za su tabbatar da cewa farashin kayayyaki sun sauko a nan gaba.
Asali: Legit.ng