'Ka Ji Tsoron Allah': Abin da Limamin Legas Ya Fadawa Tinubu a Masallacin Juma'a

'Ka Ji Tsoron Allah': Abin da Limamin Legas Ya Fadawa Tinubu a Masallacin Juma'a

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi sallar Jumu’a a Legas inda limamin masallacin ya yi masa nasiha a kan yin mulki na gaskiya
  • Sheikh Ridhwan Jamiu ya yi kira ga musulmi da su kasance masu godiya ga Allah yayin da yake yabawa kokarin shugaba Tinubu
  • Shugaba Tinubu ya samu tabbacin goyon bayan al’ummar musulmi a kokarin da yake yi na kai Najeriya zuwa tudun mun tsira

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Shugaba Bola Tinubu ya gudanar da sallar Jumu’a tare da Musulmi a babban masallacin Lekki da ke Lagos a ranar Juma’a.

Wannan ita ce fitowarsa ta farko tun bayan da ya yi sallar Juma'a a babban masallacin Alausa a makon da ya gabata.

Limamin masallacin Legas ya fadawa Tinubu gaskiya kan nauyin da ke wuyansa na shugabanci
Limamin masallacin Legas ya bukaci Tinubu ya zama shugaba adali mai gaskiya. Hoto: @muslimnews_NG
Asali: Twitter

Mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar 27 ga watan Disambar 2024.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya tona yadda ya samawa 'yan jiharsa ayyukan tarayya masu yawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya yi sallar Juma'a a Lekki

A hudubarsa, babban limamin masallacin Lekki, Sheikh Ridhwan Jamiu, ya yi kira ga mutane da su gode wa Allah cikin halin jin daɗi da rashinsa.

Ya tunatar da musulmai cewa kyakkyawan yakini da karfin imani na daga cikin halayen muminai na kwarai, musamman a lokacin wahala.

Sheikh Jamiu ya yi addu’a ga shugaba Tinubu domin samun nasara wajen jagorantar Najeriya zuwa tudun mun tsira, inda ke da zaman lafiya, tsaro da ci gaba.

Limami ya nemi a yi wa Tinubu addu'a

Limamin ya tabbatar wa shugaba Tinubu cewa al’ummar musulmi za su ci gaba da yi wa Tinubu addu’a da ba shi goyon baya a yayin mulkinsa.

Shiekh Jamiu ya ce:

“Mun yi alfahari da kai. Na tuna lokacin da muka yi kira ga mutane da su zaɓe ka a lokacin yaƙin neman zaɓe.”
“Mun san kana da ƙwarewa da basira, kuma kana da cancanta. Mun yi imani za ka cika alkawuran da ka yi domin har yanzu ba ka ba mu kunya ba.”

Kara karanta wannan

Yadda aminin Turji ke tsula tsiyarsa, wasu a yankin Sokoto sun roki gwamnati alfarma

Limamin Legas ya yi wa Tinubu nasiha

Babban limamin ya ƙara da cewa:

“Ka tuna da nauyin da ke kanka na yi wa jama’a adalci da kuma tunawa da tsayuwarka gaban Allah a ranar Lahira, inda za ka yi bayanin aikin da ka yi.”
“Manzon Allah (SAW) ya ce mafi soyuwar shugaba a wurin Allah shi ne wanda yake adalci da gaskiya.”

Shugaba Tinubu ya isa Legas domin shakatawa na bikin Kirsimeti bayan gabatar da kasafin kuɗin 2025 ga majalisar dokoki ta ƙasa a ranar 18 ga Disamba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.