An Farmaki Wata Maboyar Gaggan Barayi a Kano, an Kwato Kayan da Suka Sace

An Farmaki Wata Maboyar Gaggan Barayi a Kano, an Kwato Kayan da Suka Sace

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi nasarar kai farmaki wata maboyar barayi a karamar hukumar Danbatta
  • A yayin farmakin, 'yan sanda sun yi nasarar kwato Keke Napep da ake zargin barayin da sacewa
  • 'Yan sanda sun gurfanar da wadanda aka kama a kotu, tare da kira ga masu babura masu ƙafa uku da su kara kula

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta samu nasarar ceto babura masu ƙafa uku guda biyu da aka sace daga hannun wasu barayi.

Nasarar ta samu ne sakamakon farmakin da 'yan sanda suka kai wata maboyar barayi a ƙaramar hukumar Dambatta, a ranar 9 ga Disamba, 2024.

Napep
'Yan sanda sun kwato Keke Napep da aka sace a Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Kakakin 'yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa yadda suka mika Keke Napep din ga masu su a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

An kama gawurtaccen dan daba mai kunna riciki a unguwannin Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu baburan sun tabbatar da mallakarsu

Babur na farko mai rajista KGM 246VC, an sace shi ne bayan da wasu barayi suka sakawa matukin babur ɗin, Mamman Musa, kayan maye suka gusar masa da hankali.

Mamman ya samu kulawar likitoci a Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed kafin daga bisani a sallame shi.

An ruwaito cewa babur na biyu ma mai rajista KMC 319VK, an sace shi ne ta irin wannan hanyar farkon.

Masu baburan sun bayyana a hedikwatar ‘yan sanda, suka gabatar da shaidar mallakarsu kafin a mayar musu da baburan.

'Yan sanda sun gurfanar da masu laifi

An kama wadanda ake tuhuma da laifin su biyu, Ado Yusuf mai shekara 40 da Rabi’u Suleiman mai shekara 35.

Tuni aka gurfanar da su a gaban Kotun Majistare mai lamba 45 da ke Gyadi Gyadi a Kano, domin fuskantar hukunci.

Kira ga masu babura masu ƙafa uku

Kara karanta wannan

Jirgin yaki ya saki boma bomai a kauyukan Sokoto yana kokarin kashe Lakurawa

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kano, CP Salman Dogo Garba ya yi kira ga direbobin babura masu ƙafa uku da su kula da lafiyarsu tare da guje wa daukar fasinjojin da ba a yarda da su ba.

Rundunar ta kuma roƙi jama’a da su riƙa bayar da rahoton duk wani abu da suke zargi ta lambobin da suka bayar:

- 08032419754

- 08123821575

- 09029292926

An kama 'yan daba a jihar Kano

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan sandan jihar Kano sun samu nasarar cafke wasu matasa biyu da ake zargi da haddasa fadan daba.

Matashi na farko da aka kama ana kiransa da Awu kuma shi ake zargi da haddasa fadan daba a tsakanin unguwannin jihar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng