Ba ni kadai ba ne barawo a Najeriya, yan siyasa ne manyan barayi amma ba’a musu komai – Barawon Keke Napep
- Hukumar yan sandan jihar Neja sun damke wasu barayin Keke Napep a titin Kaduna zuwa Abuja
- Shugabansu ya bayyana rashin nadamarsa kan wannan abu
- Yace duk abinda zai faru ya faru
Jami’an hukumar SARS sun damke barayin masu suna Abbas Kabir, 19, and lmrana Abdullahi, 21 yan asalin unguwar Tudun Wada a jihar Kaduna.
Labari ya nuna cewa Kabir da Abdullahi sun saci Kake Napep guda biyu masu lamban KJ 587QA da TRN 437WSS a Zaria, jihar Kaduna.
Jaridar Northern City News ya tattaro cewa a ranan Talata, bincike mai zurfi ya taimaka wajen damke wasu abokan fashinsu 2, Ado Alhassan, 32, da Magagi Ibrahim, 21 yan asalin jihar Kano.
Abdullahi ya bayyanawa manema labarai cewa, “Yara na suna fashi a Kaduna da Kano kuma muna samun makudan kudi. Mukan zauna a manyan otel kuma mu ji dadinmu,”
Da aka tambayeshi ko ya yi nadamar abinda yake yi, Abdullahi yace, “Ban damu da duk abinda zai faru na, na riga na aikata laifin, saboda haka duk abinda zai faru ya faru. Abinda na sani shine ba ni kadai ne barawo a Najeriya ba, yan siyasa ne manyan barayi amma babu abinda ake musu.”
Kakakin hukumar yan sanda, Muhammad Abubakar, ya bayyana cewa an gano Keke Napep biyu kuma za’a gurfanar da su a kotu ba da dadewa ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng