"Kotunan Shari'ar Musulunci Sun Dade a Kasar Yarbawa," MURIC Ta Soki Gwamna
- Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Musulunci (MURIC) ta soki kalaman gwamnan Oyo, Seyi Makinde kan kotunan Musulunci
- Shugaban kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ya ce gwamnan ya na furuci ne ba tare da ilimi ko kara neman sani kan batun ba
- Farfesa Ishaq Akintola ya shawarci Kiristoci da saura mazauna kasar Yarbawa da su yi watsi da yunkurin rarraba kawunansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Oyo - Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Musulmai ta MURIC, ta soki gwamnan Oyo, Seyi Makinde bisa kalaman da ya yi a kan samar da kotun shari’ar Musulunci a jihar.
A cikin wata sanarwa da shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar a ranar Juma'a, kungiyar ta ce, Makinde ya yi magana cikin jahilci game da halin da ake ciki a ƙasa.

Source: Facebook
Daily Trust ta ruwaito kungiyar ta shawarci jami'an gwamnati su samu cikakken bayani kafin su yi tsokaci kan al'amuran da suka shafi addini da sauran muhimman batutuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Akwai kotunan shari'ar musulunci a kudu," MURIC
Muslim News Nigeria ta ruwaito Farfesa Ishaq Akintola ya ce sashe na 275(1) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 na kasa ya bayar da damar kafa kotunan shari'ah a jihohi.
Farfesa Ishaq Akintola ya kara da cewa;
“An kafa kotunan Shari'ah a ko ina cikin kasar Yarbawa. Tana cikin Legas tun daga 1993. Jihar Ogun ta sami kotunta ta Shari'ah a ranar 17 ga Janairu, 2018, kuma ya yi zaman farko a ranar 2 ga Fabrairu na shekarar 2018 a babban masallacin Egba, Kobiti, Abeokuta.”
“A rika neman ilimi a kan shari’a,” MURIC
Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta MURIC, ta shawarci gwamna Seyi Makinde da jami’an gwamnati da al’ummar Yarbawa su fahimci manufar Shari’ar musulunci.
Shugaban MURIC ya ce;
“Gwamna Makinde ya yi magana a cikin jahilci game da batun, musamman kan gaskiyar halin da ake ciki. Ya kamata jami'an gwamnati su samu cikakken bayani kafin su yi tsokaci kan al'amuran da suka shafi addini.
Gwamna ya soki kafa kotun shari'ar musulunci
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Oyo, Seyi Makinde ya yi kakkausan suka ga yunkurin wasu musulman matasan jihar na samar da kotun shari'ar addinin musulunci.
Gwamna Makinde ya bayyana cewa dokar kasa da ya ke karewa bai ba da damar samar da kotunan shari'ar Musulunci ba, amma idan har hakan na cikin doka babu matsala.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

