Lakurawa: Mazauna Kauyukan Sakkwato Suka Jawo Muka Jefa Masu Bam Inji Sojoji

Lakurawa: Mazauna Kauyukan Sakkwato Suka Jawo Muka Jefa Masu Bam Inji Sojoji

  • Rundanar sojojin kasar nan ta dora alhakin harin da aka kai kauyuka biyu a kauyen Silame da ke jihar Sakkwato
  • Shugaban Rundunar Tsaro, Janar Christopher Musa ya dora alhakin hare-haren a kan mutanen kauyukan
  • Ya ce lamarin ya shafe su ne saboda sun bayar da mafaka ga 'yan ta'adda da rundunar ke bibiya domin fatattakar su

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Shugaban Rundunar Tsaro, Janar Christopher Musa, ya gargadi 'yan kasa masu dauke da mutane da ake zargi ta’addanci.

Janar Christopher Musa laifuka da su daina irin wannan aiki ko kuma su fuskanci sakamakon ayyukansu.

Janar
Sojoji sun fadi yadda aka kai hari Sakkwato Hoto: Defense Headquarters
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito Shugaban Rundunar Tsaro hakan ne a lokacin ziyararsa ga sojojin aikin fansar yamma a Sakkwato.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Sojoji sun kashe hatsabibin shugaban ƴan bindiga da yaransa a Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun fadi dalilin kai harin Sakkwato

Shugaban Rundunar Tsaron Najeriya ya yi martani ga harin bama-bamai na ranar Kirsimeti da aka kai wa fararen hula a karamar hukumar Silame da ke jihar Sakkwato.

Janar Christopher Musa ya bayyana cewa nuna al'ummar garin ne suka fi laifi saboda zargin cewa sun ba 'yan ta'adda mafaka a cikinsu, wanda ya sa harin ya shafe su.

Dakarun Sojoji sun ja kunnen ‘yan ta’adda

Rundunar sojojin kasar nan ta ce ba za ta zuba idanu ‘yan ta’adda su na cin karensu babu babbaka a kasar nan tare da hana jama'a zaman lafiya ba.

Ya ce haka kuma ba za su daga kafa ga duk wanda aka kama ya na ba wa ‘yan ta’addan mafaka ba, yayin da sojoji ke cigaba da ayyukansu na kakkabe ta'addanci.

Sojoji sun kai hari Sakkwato

A wani labarin, kun ji cewa sojojin saman kasar nan sun kai hare-haren bama-bamai a kan wasu kauyuka biyu da ke Sakkwato, inda aka hallaka mutane akalla 10 tare da jikkata wasu da dama.

Kara karanta wannan

NAF: Rundunar sojin sama ta yi magana kan rahoton kuskuren kashe bayin Allah a Sokoto

Rundunar soja ta bayyana cewa dakarunta na 'Operation Fansar Yamma' sun kai sumame kan wasu 'yan ta'adda da ake zargin 'yan kungiyar Lakurawa ne da ke zaune a yankunan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.