'Mu ba Yan Ta'adda ba ne': Bello Turji Ya Kalubalanci Sojoji, Ya Tabo Gwamna Dauda
- Kasurgumin dan ta'adda, Bello Turji ya soki hukumomin Najeriya kan yada karya da cewa sun kama yan uwansa
- Turji ya ce sojoji suna ba yan Najeriya kunya saboda sun je sun kama dattawa a asibitoci amma suna cewa sun kama yan bindiga
- Dan ta'addan ya dawo kan Gwamna Dauda Lawal Dare inda ya ce ya hana Zamfara zaman lafiya gaba daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Kwanaki kadan bayan cafke wasu da ake zargin mataimakan Bello Turji ne, dan ta'addan ya yi martani.
Bello Turji ya soki hukumomin Najeriya kan abin da ya kira karairayinsu game da yada cewa an kama wasu daga cikin yan uwansa.
Bello Turji ya caccaki sojojin Najeriya
Hakan na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo da Malam Murtala Bello Asada ya wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan ta'addan ya ce abin kunya ne sojoji suna yada kama mataimakansa inda ya ce kawai wasu dattawa suka kama.
A cikin faifan bidiyo, Turji ya kalubanci Gwamna Dauda Lawal kan alfahari da ya yi game da ta'addanci a jihar Zamfara.
Dan ta'addan ya kara tabbatar wa Dauda Lawal cewa su ba yan ta'adda ba ne, a bar danganta su da haka.
Turji ya ce su ba yan ta'adda ba ne
"Mun ji shugaban sojojin ka fito kana cewa ka fatattaki yan ta'adda, ka ba yan Najeriya kunya wallahi, a ina ka yi ba ta-kashi? Ka fada!"
"A Zamfara da Sokoto da muke kake fada masa wannan magana, ka kama uwayenmu da dattawa wasu sun kai shekaru 75 amma ka dube ni dan shekara 35 ka ce ka kama mataimaka na."
"Kai kuma Gwamna Dauda Lawal ka ce sai dan ta'adda ya ji wuta ya ba ka bingida, ai mu dama ba yan ta'adda ba ne, ku kuka bata masa suna."
- Bello Turji
Bello Turji ya sha alwashin kai hare-hare
Mun ba ku labarin cewa dan ta'adda, Bello Turji ya sake fitar da wani bidiyo inda yake gargadin hukumomin Najeriya.
A cikin bidiyon, Turji ya bukaci hukumomi su sako musu yan uwansu ko kuma su fuskanci munanan hare-hare a sabuwar shekarar 2025.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng