"Kasa da 15000": Kwankwaso Ya Fadi Yawan Kuri'un da Yake So APC Ta Samu a Kano a 2027
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce NNPP za ta rage tasirin APC a Kano, kuma ba za ta samu sama da kuri’u 15,000 a 2027 ba
- Idan za a iya tunawa, NNPP ta samu kuri’u sama da miliyan daya, yayin da APC ta samu kuri'u 890,705 a zaben Kano na 2023
- Dan takarar shugaban kasar ya fadi matakan da jam'iyyar NNPP za ta dauka domin samun nasara a 2027 da kuma gurgunta APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano, ya ce jam'iyyar NNPP za ta rage tasirin APC a jihar nan da zaben 2027.
Yayin taron masu ruwa da tsaki na NNPP a Tsanyawa, Kwankwaso ya ce APC ba za ta samu sama da kuri’u 15,000 a zaben 2027 ba.
"NNPP za ta rage tasirin APC a Kano" - Kwankwaso
A zaben 2023, NNPP ta samu kuri’u 1,019,602, APC ta samu 890,705, PDP kuma ta tsaya zo a uku da kuri’u 15,957 a jihar Kano, a cewar rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwankwaso ya ce samun kuri’u sama da miliyan daya a matsayin sabuwar jam’iyya alama ce ta nasara duk da ƙarancin lokacin yakin neman zabe.
"Yanzu lokaci ne na rage tasirin APC. Za mu tabbatar da cewa kuri’unsu sun ba su haura 15,000 a 2027 ba."
- A cewar Kwankwaso.
Kwankwaso ya hango nasarar NNPP a 2027
Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce NNPP za ta ci gaba da karfafa yakin neman zabe, tare da tabbatar da nasarar jam’iyyar a zabukan da ke tafe.
A matsayin dan takarar shugaban kasa na NNPP a 2023, Kwankwaso ya bukaci magoya baya da su kasance tsintsiya madaurinki daya wajen samun nasarar jam'iyyar.
Kwankwaso ya kuma jaddada cewa hadin kai da dagewa su ne makamin nasara ga NNPP a duk fadin Najeriya kuma hakan zai ba ta nasara a 2027.
APC ta yi martani ga kalaman Kwankwaso
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar APC ta yi wa Sanata Rabi Musa Kwankwaso wankin babban bargo kan wasu kalamai da ya yi a kan zaben 2027.
Maimaikon ya rika hasashen abin da ba zai iya faruwa a 2027 ba, APC ta bukaci Kwankwaso da ya mayar da hankali kan ganin ya zama cikakken dan NNPP.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng