"Kalaman Tchiani Sun ba Mu Mamaki," Najeriya Ta Karyata Hannu a Matsalolin Nijar
- Gwamnatin Najeriya ta musanta zargin da Nijar ta yi na cewa ana hada baki da ita wajen kokarin jefa hargitsi kasar
- A ranar Alhamis ne aka ga shugaban soja na Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya na fadin cewa Najeriya na cutar da ita
- A martanin Najeriya, mashawarcin shugaban kasa a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya ce babu kamshin gaskiya a zargin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Zarge-zargen da gwamnatin sojan Nijar ta yi wa Najeriya ya tayar da kura, bayan shugaba Janar Abdourahamane Tchiani da zargin Najeriya ta karbi kwagilar lalata kasarsa.
Tun a ranar Alhamis da labarin ya fita, mukarraban gwamnatin Bola Ahmed Tinubu su ka rika karyata zargin, tare da jaddada matsayar Najeriya na yaki da ta'addanci.
BBC Hausa ta ruwaito mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya bayyana mamakin irin girman zargin da Nijar ta fito duniya ta na yi wa Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Najeriya ta karyata zargin shugaban kasar Nijar
Mashawarcin Tinubu ya bayyana mamakin yadda shugaban Nijar ya zargi Najeriya da hada kai da Faransa domin jefa hargitsi a cikin Nijar.
Nuhu Ribadu ya ce;
"Abin ya zo mana da tayar da hankali da hankali da mamaki da mai girma shugaban Nijar ya fada, ba ta da tushe, ba gaskiya. Najeriya ba za ta taba yi wa Nijar zagon kasa ba.
"Najeriya ba za ta taba yadda masifa ta fada wa Nijar ba, Najeriya ba ta da fitina ko rashin zaman lafiya da makotanmu."
"Dukkan mu muna zaune lafiya da Kamaru, muna zaman lafiya da Chad, muna zaman lafiya da Benin. Ya za a yi a ce kuma mun samu matsala da Nijar, ta ina?"
Najeriya ta musanta ba sojojin Faransa mafaka
Gwamnatin Najeriya ta ce babu gaskiya a cikin zargin da Nijar ke yi mata na ba sojojin Faransa makafa domin a samu damar yakarta da jefa mata hargitsi.
Mashawarcin shugaban kasa, Nuhu Ribadu ya ce;
"Najeriya ba ta da wannan tarihi na ba wa kasashen waje dama su zo su zauna a kasarta. Ingila da kanta da su ka yi mana mulkin mallaka ba su taba, ko sau daya su ce za su kawo mana sojojinsu su zauna."
"Amurka babu yadda ba ta yi ba, ba mu yadda ba, daga baya su ka je wajen Nijar, Nijar ta ba su dama kafin daga baya su kore su."
Ya ce bai dace saboda Nijar na fada da Faransa, ya zama dole sai kasar nan ta shiga takun saka da kasar ba.
Nijar ta zargi Najeriya da zagon kasa
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban kasar Nijar, Abdourahamane Tchiani ya bayyana cewa Najeriya ta hada baki da Faransa a wajen kokarin haddasa fitintunu a jamhuriyyar.
Janar Tchiani ya bayyana cewa yanzu haka Faransa da ISWAP sun rattaba hannu a kan wata yarjejeniya da ta kafa Lakurawa a wasu sassan Najeriya domin saukaka kai masu farmaki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng